Daga Wakilanmu
Wasu takardun kotu da Katsina Times ta samu daga Babbar Kotun Jihar Katsina karkashin Mai Shari'a A. A. Abdullahi, sun nuna cewa an aika da takardar tuhumar raina kotu ga wasu shugabannin Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina.
Takardun sun nuna cewa tuhumar ta samo asali ne daga wata shari'a da Alhaji Jibrin Tanimu ya shigar a gaban kotu, inda ya ke ƙara wasu jami'an Hisbah guda uku, Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina da kuma Babbar Lauyar Gwamnatin Jihar Katsina.
Wata takarda da Katsina Times ta gani ta bayyana cewa an ambaci sunan Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina kan wasu hujjojin da ake zargin sun nuna rashin bin umarnin kotu.
Takardar ta ce idan kotu ta tabbatar da zargin raina kotu, hakan na iya jawo hukuncin da ya haɗa da tura wanda ake tuhuma gidan gyaran hali.
Haka kuma, wata takarda ta daban ta nuna cewa kin amsa gayyatar kotu da ake zargin shugaban hukumar ya yi na daga cikin dalilan da ake kallon a matsayin raina kotu.
Da Katsina Times ta nemi jin ta bakin Hukumar Hisbah kan lamarin, ba a samu wata amsa a hukumance ba. Sai dai wani jami'in hukumar, wanda ya nemi a sakaya sunansa, ya tabbatar cewa an karɓi takardun tuhumar raina kotun, ciki har da wadda ta shafi Shugaban Hukumar Hisbah ta Jihar Katsina, Dakta Abu Ammar.
Jami'in ya ce ba za su yi wani ƙarin bayani kan lamarin ba a halin yanzu, saboda shari'ar na gaban kotu.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page.katsina city news
Jaridar Taskar labarai.,Katsina City News
Katsina times @ All social media handles


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!