Cikakken Rahoton: 'Yan Sanda Sun Tsare Dakta Bashir Kurfi

Daga Mu'azu HassanA yau Talata da misalin karfe 1:00 na rana ne aka gayyaci Dakta Bashir Kurfi zuwa Hedikwatar Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina domin amsa wasu tambayoyi kan wasu…

Katsina City News July 07, 2026  ·  12:00 AM
| 116 Views
Cikakken Rahoton: 'Yan Sanda Sun Tsare Dakta Bashir Kurfi
Cikakken Rahoton: 'Yan Sanda Sun Tsare Dakta Bashir Kurfi

Daga Mu'azu Hassan

A yau Talata da misalin karfe 1:00 na rana ne aka gayyaci Dakta Bashir Kurfi zuwa Hedikwatar Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina domin amsa wasu tambayoyi kan wasu batutuwa.

Rahotanni sun ce, da isar sa hedikwatar, jami'an 'yan sanda sun fara yi masa tambayoyi ne kan wasu korafe-korafe da suka shafi Karamar Hukumar Kurfi, wadanda kungiyar Network for Justice, karkashin jagorancinsa, ke bibiya.

Bayan ya kammala bayar da bayanan da ake bukata, yana shirin tafiya ne jami'an 'yan sanda suka sanar da shi cewa akwai wani korafi da aka shigar a kansa dangane da wata hira da ya yi da gidan talabijin na Daily Trust TV. A cikin hirar, ya yi ikirarin cewa ana zargin Gwamnatin Jihar Katsina da daukar nauyin wasu tsoffin 'yan bindiga da aka yi sulhu da su zuwa aikin Hajjin bana.

Da yake zantawa da Katsina Times a Hedikwatar Rundunar 'Yan Sandan Jihar Katsina, Dakta Bashir Kurfi ya ce an ba shi takardar korafin domin ya karanta, sannan aka sanar da shi cewa za a fara yi masa tambayoyi a kanta. 

Sai dai ya bayyana wa jami'an cewa ba zai yi wata magana ba har sai lauyoyinsa sun iso.

Ya kara da cewa da misalin karfe 4:00 na yamma aka dauke shi zuwa kotu, amma da isar su sai suka tarar an riga an tashi zaman kotun, lamarin da ya sa aka mayar da shi hedikwatar 'yan sanda.

Kurfi ya ce har zuwa lokacin da wakilan Katsina Times suka ziyarce shi, ana ci gaba da tsare da shi a wani ofishi cikin mutunci, ba tare da cin zarafi ko musgunawa ba.

Ana sa ran a ranar Laraba za a gurfanar da Dakta Bashir Kurfi a gaban kotu, domin a cewarsa jami'an 'yan sanda sun shaida masa cewa ba za su ci gaba da tsare shi fiye da awanni 24 ba.

Advertisement

A kwanakin baya ne Dakta Bashir Kurfi ya yi hira da Daily Trust TV, inda ya yi ikirarin cewa ana zargin Gwamnatin Jihar Katsina da daukar nauyin wasu tsoffin 'yan bindiga da aka yi sulhu da su zuwa aikin Hajjin bana. Wannan ikirari ya bazu a kafafen yada labarai na cikin gida da na kasashen waje.

Sai dai Gwamnatin Jihar Katsina ta musanta zargin, tare da bayyana cewa ba shi da tushe.

Haka kuma gwamnatin ta yi alkawarin daukar matakin shari'a idan ba a gabatar da hujjoji da ke tabbatar da zargin ba ko kuma ba a janye shi ba.

Katsina times 

Www.katsinatimes.com 

Facebook page : Katsina city News 

Facebook page; jaridar taskar labarai 

07043777779.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 5 + 2?