An Dakile Harin ’Yan Bindiga a Bakori

Daga WakilanmuMafarauta da jami’an tsaron CWG sun yi nasarar dakile wani yunkurin kai hari da wasu ’yan bindiga suka yi a ƙauyen Gidan Bawa, da ke Ƙaramar Hukumar Bakori, a…

Katsina City News August 19, 2026  ·  12:00 AM
| 42 Views
An Dakile Harin ’Yan Bindiga a Bakori
An Dakile Harin ’Yan Bindiga a Bakori

Daga Wakilanmu

Mafarauta da jami’an tsaron CWG sun yi nasarar dakile wani yunkurin kai hari da wasu ’yan bindiga suka yi a ƙauyen Gidan Bawa, da ke Ƙaramar Hukumar Bakori, a daren Talata, 18 ga watan Agusta, 2026.


Rahotanni sun ce ’yan bindigar, waɗanda ake zargin suna ƙarƙashin jagorancin wani da ake kira Isiya Kwashen Garwa, kimanin 40 ne, suka shiga ƙauyen Gidan Bawa da ke yankin Kandrawa, inda suka kama mutane 45, mafi yawansu mata da yara, da nufin yin awon gaba da su zuwa cikin daji.


Sai dai jami’an Mafarauta, jami’an tsaron CWG da wasu jami’an Civilian JTF da ke sansanin Guga sun yi wa ’yan bindigar kwantan bauna yayin da suke ƙoƙarin barin ƙauyen.


Advertisement

NRS Gateway

A yayin musayar wuta, jami’an tsaron sun yi nasarar kashe ’yan bindiga bakwai tare da kuɓutar da mutane 34 daga cikin waɗanda aka yi garkuwa da su.


Sai dai mutane uku daga cikin waɗanda aka yi yunƙurin sacewa sun rasa rayukansu sakamakon musayar wutar, yayin da wasu mutane biyar suka ɓace. Ana zargin cewa wasu daga cikinsu sun tsere, ko kuma ’yan bindigar sun yi nasarar tafiya da su.


A yayin fafatawar, jami’an tsaron sun kuma kwato shanu 19 da wasu kayayyaki da ’yan bindigar suka sata lokacin da suka shiga ƙauyen Gidan Bawa.


Hukumomin tsaro na ci gaba da bincike domin gano inda mutanen da suka ɓace suke da kuma bibiyar sauran ’yan bindigar da suka tsere.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 7?