Bincike: Wasu Attajirai da Kamfanoni a Katsina ana Zarginsu da Kin Biyan Haraji ,Yadda Doka Ta Tanada

Daga Mu'azu Hassan, Katsina TimesWani bincike da Katsina Times ta gudanar kan tsarin tattara haraji a Jihar Katsina ya gano abin da ke nuna cewa wasu daga cikin attajiran jihar…

Katsina City News June 30, 2026  ·  12:00 AM
| 49 Views
Bincike: Wasu Attajirai da Kamfanoni a Katsina ana Zarginsu da Kin Biyan Haraji ,Yadda Doka Ta Tanada
Bincike: Wasu Attajirai da Kamfanoni a Katsina ana Zarginsu da Kin Biyan Haraji ,Yadda Doka Ta Tanada

Daga Mu'azu Hassan, Katsina Times

Wani bincike da Katsina Times ta gudanar kan tsarin tattara haraji a Jihar Katsina ya gano abin da ke nuna cewa wasu daga cikin attajiran jihar da wasu kamfanoni masu zaman kansu ba sa biyan haraji yadda doka ta tanada.


A yayin binciken, jaridar ta yi nazarin wasu takardun da suka shafi biyan haraji na wasu kamfanoni da manyan shaguna da ke gudanar da harkokin kasuwanci masu dimbin kudaden shiga da kuma riba mai yawa.


Binciken ya nuna cewa akwai wasu manyan shaguna da ake kyautata zaton ribar su ta shekara na kai daruruwan miliyoyin naira, amma adadin harajin da ake bayyana sun biya a karshen shekara bai yi daidai da girman kasuwancinsu ba.


Haka kuma, binciken ya gano cewa wasu manyan gonakin noma da kiwo da ake kyautata zaton kudaden shigarsu na kai daruruwan miliyoyin naira a shekara suna biyan harajin da wasu ke ganin bai dace da irin kasuwancin da suke yi ba.


Wani abin da ya dauki hankali a binciken shi ne cewa, a wasu lokuta, harajin da ake cire wa ma'aikacin gwamnati mai mataki na 10 a shekara ya fi harajin da ake zargin wasu masu manyan otal-otal da harkokin kasuwanci a Katsina ke biya.


Wasu ginannun kamfanonin a katsina, binciken mu ya gano a maimakon su biya haraji, sai su kare da korafin faduwa sukayi.


Binciken mu ya gano da ace attajiran katsina , shaguna da kamfanoni, otel otel da sauransu zasu biya haraji ga gwamnatin jaha da kudin shiga sun kara karfi a jahar.

Advertisement


Binciken mu ya gano jahar katsina ce koma baya wajen biyan harajin kamfanoni da masu kudi a tsakanin jihohi tsararrakin ta.


Sai dai binciken ya nuna cewa mafi yawan 'yan kwangilar gwamnati ba sa kauce wa biyan haraji, kasancewar gwamnati kan cire harajin kai tsaye daga kudaden kwangilar da take biya kafin a mika musu ragowar kudin.


Katsina Times ta yi kokarin jin ta bakin Hukumar Tara Haraji ta Jihar Katsina da kuma wasu daga cikin kamfanoni da mutanen da binciken ya shafa domin samun karin haske kan batun. Har zuwa lokacin hada wannan rahoto, ba a samu amsarsu ba.


Jaridar za ta ci gaba da bibiyar lamarin tare da wallafa duk wata amsa ko karin bayani daga bangarorin da abin ya shafa.


Katsina times 

@ www.katsinatimes.com 

Facebook page; katsina city news 

Jaridar Taskar labarai @ Facebook page.

07043777779.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 4 + 6?