Gwamnatin Katsina Hadin Gwiwa Da ABUCONS Ta Shirya Horaswa Ta Kwana Biyu Kan Inganta Tsarin Saye da Gudanar da Ayyukan Gine-gine

Zaharadeen Ishaq Abubakar | Katsina Times Gwamnatin Jihar Katsina ta hannun Hukumar Katsina State Development Management Board (KTDMB), tare da haɗin gwiwar Ahmadu Bello University Consultancy Services (ABUCONS) ta gudanar da…

Katsina City News July 19, 2026  ·  12:00 AM
| 65 Views
Gwamnatin Katsina Hadin Gwiwa Da ABUCONS Ta Shirya Horaswa Ta Kwana Biyu Kan Inganta Tsarin Saye da Gudanar da Ayyukan Gine-gine
Gwamnatin Katsina Hadin Gwiwa Da ABUCONS Ta Shirya Horaswa Ta Kwana Biyu Kan Inganta Tsarin Saye da Gudanar da Ayyukan Gine-gine


Zaharadeen Ishaq Abubakar | Katsina Times 


Gwamnatin Jihar Katsina ta hannun Hukumar Katsina State Development Management Board (KTDMB), tare da haɗin gwiwar Ahmadu Bello University Consultancy Services (ABUCONS) ta gudanar da taron horaswa na kwana biyu ranar asabar 18 da lahadi 19 ga watan juni 2026, kan Tsarin Ingancin Aiki (Total Quality Management – TQM), Binciken Farashi (Price Intelligence) da Daidaita Kasafin Kuɗin Ayyukan Gine-gine, domin ƙarfafa ƙwarewar jami’an gwamnati da ke kula da ayyukan raya ƙasa da tsarin saye.


An gudanar da taron Horaswar a Tahir Guest Palace da ke Kano, inda injiniyoyi, masu ƙididdigar gine-gine (Quantity Surveyors), jami’an saye, masu sa ido kan ayyuka da sauran manyan jami’an gwamnati daga ma’aikatu da hukumomin jihar suka halarta.


Da yake jawabi a wajen buɗe taron, Babban Sakataren KTDMB, Dakta Mustapha Shehu, ya ce horaswar na daga cikin matakan da gwamnatin jihar ke ɗauka domin inganta ƙwarewar ma’aikata, tabbatar da gaskiya da inganci wajen aiwatar da ayyukan gwamnati.


Ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta amince a riƙa gudanar da irin wannan bita sau uku a shekara domin tantance ƙalubalen da ake fuskanta da kuma samar da hanyoyin magance su.


Advertisement

BSIL Security Report

Ya kuma ce a nan gaba za a duba yadda za a yi amfani da Basirar Wucin-gadi (Artificial Intelligence – AI) cikin bin ƙa’idojin aiki wajen shirya takardun fasaha da gudanar da ayyukan gine-gine.


Taron ya samu halartar Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri, Injiniya Dakta Sani Magaji Ingawa; Darakta Janar na Hukumar Saye da Kwangila ta Jihar Katsina, Alhaji Badamasi Ya'u Yantumaki; Mai Bai Wa Gwamna Shawara kan Tsare-tsare da Bibiyar Ayyuka (SPIME), Aminu Ibrahim Ida; da Mai Bai Wa Gwamna Shawara kan Gyaran Aikin Gwamnati, Alhaji Usman Isyaku, wanda ya ayyana taron a hukumance.


A nasa muƙalar buɗe taron, Manajan Darakta na ABUCONS, Farfesa M. Dodo, ya yi bayani kan muhimmancin daidaita ƙididdigar kuɗin ayyuka da tabbatar da inganci domin samar da ayyukan gine-gine masu ɗorewa da amfani ga al'umma.


Haka kuma, ƙwararren masani kan fasahar sadarwa na ABUCONS, Ismail Abbas, ya gabatar da sabuwar manhajar zamani da za ta taimaka wajen ƙididdigar farashi, kula da inganci da gudanar da ayyukan gine-gine.


A nasa jawabin godiya, Babban Daraktan Sashen Ababen More Rayuwa na KTDMB, Farfesa Jamilu Usman, ya yaba wa gwamnatin Jihar Katsina da ABUCONS bisa shirya wannan shiri, yana mai cewa zai taimaka wajen inganta tsarin saye da aiwatar da ayyukan raya ƙasa a jihar.


Wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana horaswar a matsayin wadda ta zo a kan lokaci, suna masu cewa za ta ƙara musu ƙwarewa wajen sa ido kan ayyukan gwamnati, rage almubazzaranci da tabbatar da inganci da amfani da kuɗin jama'a yadda ya kamata.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 4 + 4?