Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Ayyukan Tituna na Naira Biliyan 6.4 a Funtua

Daga Wakilin mu Funtua, Jihar Katsina Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da wasu manyan ayyukan tituna guda biyu da aka kashe kimanin Naira biliyan 6.4 wajen aiwatar…

Katsina City News July 21, 2026  ·  12:00 AM
| 20 Views
Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Ayyukan Tituna na Naira Biliyan 6.4 a Funtua
Gwamna Radda Ya Ƙaddamar da Ayyukan Tituna na Naira Biliyan 6.4 a Funtua

Daga Wakilin mu Funtua, Jihar Katsina 

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya ƙaddamar da wasu manyan ayyukan tituna guda biyu da aka kashe kimanin Naira biliyan 6.4 wajen aiwatar da su a garin Funtua, inda ya ce ayyukan na nuna ƙudirin gwamnatinsa na inganta ababen more rayuwa, bunƙasa tattalin arziki da kuma tabbatar da tsaron masu amfani da ababen hawa.


Ayyukan sun haɗa da sake ginawa tare da faɗaɗa titin Funtua–Katsina mai tsawon kilomita 3.9, wanda aka kashe Naira biliyan 5.8, da kuma gyara tare da inganta titin Tsohuwar Kasuwa mai tsawon kilomita 1.2, wanda ya lakume kudi Naira miliyan 637.


Da yake jawabi a wajen ƙaddamar da ayyukan ranar Talata, Gwamna Radda ya bayyana cewa ayyukan na daga cikin shirin Sabunta Birane (Urban Renewal Programme) da gwamnatinsa ke aiwatarwa domin inganta ababen more rayuwa a faɗin jihar.


Ya ce sabbin titunan za su sauƙaƙa zirga-zirga, rage lokacin tafiya, ƙara tsaron masu amfani da hanya tare da bunƙasa harkokin kasuwanci a Funtua da kewaye.


Gwamnan ya bayyana cewa an girka fitilun tituna masu amfani da hasken rana a kan hanyoyin domin ƙarfafa tsaro, kare lafiyar al'umma da kuma ƙawata muhallin birnin.


Ya ƙara da cewa kamfanin Mothercat Limited ne ya aiwatar da ayyukan ƙarƙashin kulawar Ma'aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta Jihar Katsina, a matsayin wani ɓangare na shirin sabunta birane da ake gudanarwa a shiyyoyin Sanatan Katsina, Daura da Funtua.


Advertisement

BSIL Security Report

Gwamna Radda ya ce kammala ayyukan na nuna jajircewar gwamnatinsa wajen samar da ingantattun ababen more rayuwa da za su tallafa wa ci gaban tattalin arziki da inganta rayuwar al'umma.


Ya kuma yaba wa Ma'aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri bisa yadda ta sa ido kan ayyukan, tare da jinjinawa kamfanin Mothercat Limited saboda kammala su bisa ƙa'idojin aikin injiniya. Haka kuma ya gode wa al'ummar Funtua kan haƙurin da suka yi a lokacin gudanar da ayyukan.


Tun da farko, Kwamishinan Ayyuka, Gidaje da Sufuri, Engr. Sani Magaji Ingawa, ya ce ƙaddamar da titunan wata muhimmiyar nasara ce ga shirin sabunta biranen da gwamnatin Radda ke aiwatarwa.


Ya bayyana cewa titin Funtua–Katsina ya taso daga Madauwar Babban Masallacin Juma'a zuwa Madauwar Dutsen Rimi, yayin da titin Tsohuwar Kasuwa ya haɗa Madauwar Babban Masallacin Juma'a da hanyar Zariya–Gusau Bypass.


A cewarsa, an gina titunan ne da kwalta mai inganci tare da girka fitilun tituna masu amfani da hasken rana, bisa mafi girman ƙa'idojin aikin injiniya da manufofin tabbatar da ingancin ayyukan gwamnatin jihar.


Ingawa ya tunatar da cewa Gwamna Radda ya ƙaddamar da manyan ayyukan tituna uku a Funtua a bara, yana mai bayyana cewa aikin titin Sokoto Road na ci gaba yadda ya kamata, kuma ana sa ran kammala shi tare da ƙaddamar da shi kafin ƙarshen shekarar 2026.


Taron ƙaddamar da ayyukan ya samu halartar Hakimin Funtua kuma Sarkin Maskan Katsina, Alhaji Sambo Idris Sambo, Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Katsina, Hon. Nasir Yahaya Daura, Shugaban Ma'aikatan Gwamna, Hon. Abdulkadir Mamman Nasir, Babban Sakataren Gwamna mai zaman kansa, Hon. Abdullahi Aliyu Turaji, da mambobin Majalisun Dokoki na Tarayya da Jiha, sarakunan gargajiya, shugabannin addinai da sauran manyan jami'an gwamnati.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 3?