TARIHIN POLO A KATSINA.
- Katsina City News
- 22 Dec, 2024
- 73
Tarihi ya nuna an Fara wasan Polo a Katsina acikin shekarar 1924, Mr. S. J Hogben shine ya kafa tushen wannan wasan. Alokacin mulkin Sarkin Katsina Alhaji Muhammadu Dikko(1906-1944). Da farko Sarkin Katsina Muhammadu Dikko shi ya fara daukar dawainiyar wasan Polo a Katsina,shike sayen kaya daga aljihunsa, da Dawaki, da Sirada da Sandunan Kwallo da Kwallayen. Daga baya wata Kungiyar wasan Polo Mai suna " Katsina Polo Club" suka ci gaba da daukar dawainiyar wasan Polon a Katsina, Wanda Yan wasan suka rika bada gudunmuwa a tsakanin su, Kuma baitulmali ta rika yin taimako.
Cikin dan lokaci Kungiyar Polo ta Katsina Mai suna " Katsina Polo Club" tayi zarra aduk fadin Afirika wajen Wasan Polo. Cikin dan lokaci tayi nasarar cin manyan Kofuna na wasan Polo da suka hada da Geogiion Cup, Nigerian Cup, Emir of Katsina Cup, da sauransu. Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo shine Kaftin na farko na Kungiyar Polo ta " Katsina Polo Club". Hakanan kuma Alhaji Sir Usman Nagogo shine zakaran farko na wasan Polo a Tarayyar Nigeria, yana da Handicap plus 7.
Katsina ta fitar da gwanayen Yan wasan Polo na farko da suka hada da Sarkin Katsina Alhaji Sir Usman Nagogo Wanda yayi ritaya daga wasan Polo da Handicap +7. Akwai Alhaji Yusuf Lamba Handicap +3, Dandada Handicap +3, da sauransu.
Sauran Yan wasan Polo na Katsina sun hada da Marigayi Sarkin Katsina Alhaji Dr. Muhammad Kabir Usman, Janar Hassan Katsina, Alhaji Abdu Usman( Majidadi), Alhaji Sani Saulawa, Sanusi Kabir, Ummaru Kabir ( Malam), Bashir Mangal, Dahiru Usman Sarki da sauransu.
WASU KOFUNA DA KUNGIYAR POLO TA KATSINA TAYI NASARA AKAN SU, WADANDA HAR YANZU SUNA A DAKIN KWAF DAKE GIDAN SARKI.
1. Nigerian Polo Association Cup((1938)
2. Katsina Polo Association Cup (1938)
3. Georgian Tropy (1949).
4. Georgian Cup (1959)
5. Wazirin Gwandu Alhaji Ummaru's Cup ( 1980)
6. Independence Cup ( 1962)
7. Racca Cup
8. Appreciation Moment for Nigeria vs India Polo Tournament.
Alh. Musa Gambo Kofar soro.