GWAMNA LAWAL YA RATTABA HANNU KAN KASAFIN KUƊIN NAIRA BILIYAN 546 NA SHEKARAR 2025, YA SAKE ƊAUKAR ALƘAWARIN CETO JIHAR ZAMFARA
- Katsina City News
- 21 Dec, 2024
- 82
Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal ya rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗin shekarar 2025 na Naira 546,014,575,000.00.
Kasafin kuɗin 2025 mai taken; “Kasafin Ceto 2.0”, kakakin majalisar dokokin jihar Zamfara ya gabatar wa gwamnan a ranar Alhamis a gidan gwamnatin jihar da ke Gusau.
A yayin rattaba hannu kan ƙudirin kasafin kuɗi na shekarar 2025, Gwamna Lawal ya ƙuduri aniyar kammala dukkan ayyukan da ake gudanarwa tare da inganta nasarorin da aka samu a cikin watanni 18 da gwamnatinsa ta yi.
Gwamnan ya bayyana muhimmancin kasafin kuɗin shekarar 2025, inda ya ce ‘ba wai kawai mu kalli inda muke ko kuma inda muka dosa ba, amma inda muka kasance’.
“Abin ya tsananta a bara. Shekaru goma na rashin shugabanci nagari ya haifar da durƙushewar tattalin arziki, rashin biyan ma'aikatan gwamnati albashi, da kuma basussukan da ke kawo cikas ga ilimin yara. An lalata ababen more rayuwa, an yi watsi da asibitoci, kuma ayyukan jama'a sun ɗaiɗaita. Bugu da qari kuma, akwai rashin bin doka da oda, da batun kuɗin wutar lantarki da ake ci gaba da yi, da rashin isasshen ruwan sha, rashin tsaro, da ƙaruwar cututtuka masu yaɗuwa kamar kwalara, tare da raguwar kuɗaɗen shiga na cikin gida.
“Da ba mu yi gaggawar magance dukkan ƙalubalen ba, da jihar Zamfara ba za ta zama wurin da dukkan mu za mu iya rayuwa a yau ba.
“Ƙudirin Ceto na 2025 2.0 yana gudana ne ta hanyar jajircewarmu na ci gaba da ayyukan da muka fara wa mutanenmu, wanda ke nuna kyawawan manufofi na kishi. Wannan kasafin kuɗin kuma ya sanya aka ƙara wa ma’aikata ƙarin albashi mafi ƙaranci, inda ya tashi daga N30,000 zuwa N70,000.
Gwamna Lawal ya bayyana cewa lokaci ya yi da jihar Zamfara za ta shawo kan lalacewar ababen more rayuwa da kuma ƙoƙarin inganta gine-gine.
Kasafin kuɗin 2025 zai shafi gudanar da ayyukan filin jirgin sama na Gusau da kuma aikin gina hanyar Gusau-Magami zuwa Dansadau.
“Hakazalika, Kasafin 2025 zai shafi samar da kayan aikin tsaro ta hanyar ‘Asusun Tsaro’, gina makarantu ta hanyar shirin Agile, kafa cibiyar bincike ta zamani, gina birnin na zamani, samar da abinci a ƙarƙashin shirin Fadama III, sauƙin kasuwanci ta hanyar 'Saber Program', gyara Cibiyar Bafarawa Shinkafi, da gina Cibiyar Taro ta Duniya.
“Aikin gina titin Lalan zuwa Lalan, inganta asibitin ƙwararru na Yariman Bakura zuwa asibitin koyarwa, gina ƙarin gine-gine a manyan asibitocin Anka, Kauran namoda, Gummi, Shinkafi, Magami, Tsafe, Jangebe, da Bukkuyum, inganta wuraren kwanan 'yan gudun hijira ta hanyar shirin Solid, haɓaka yawan amfani da dabbobi ta hanyar shirin L-Press, gina hanyar mai nisan kilomita 126 daga magami-dangulbi-dankurmi-bagega-anka.”
Sauran ayyukan da za a ƙaddamar a cikin kasafin kuɗin 2025 sun haɗa da shirin NG-Cares na ƙarfafa ci gaban al’umma, gina cibiyar wasanni ta Gusau, gina titin Mallamawa – Zarummai – Bukkuyyum, gina sabuwar makarantar koyon aikin jinya da ungozoma ta Zurmi, kammalawa Cibiyar Siyayya ta Gusau da ke tsohon wurin shaƙatawa, da kuma gina titin kilomita 94 a Yandoton Daji-Doka-Yanwaren-daji-Hayin alhaji-Bedi-Yankuzo-Tsafe.
Sulaiman Bala Idris
Mai magana da yawun Gwamnan jihar Zamfar
Disamba 19, 2024