DSS ta kama Mahdi Shehu kan bidiyo na bogi
- Katsina City News
- 30 Dec, 2024
- 93
Hukumar Tsaro ta Ƙasa (DSS) ta kama fitaccen ɗan gwagwarmaya, Mahdi Shehu, a ƙarshen mako.
Bayanan yadda aka kama shi ba su fito fili ba, amma jaridar News Diary ta yanar gizo ta gano cewa yana tsare a Kaduna.
News Diary Online ta kuma gano cewa DSS ta kama Mahdi Shehu ne bisa zarginsa da alaka da wani bidiyo na bogi kan batun tsaro na ƙasa wanda ya bazu a kafafen sada zumunta.
Majiyoyi sun bayyana cewa DSS ba ta yi gaggawar kama shi ba saboda jami’an hukumar sun yi muhawara da Mahdi kan bidiyon da aka tabbatar ba gaskiya ba ne. Sai dai duk ƙoƙarin DSS na warware lamarin bidiyon ya ci tura, wanda hakan ya sa aka kama shi.
Majiyoyi sun shaida wa News Diary Online cewa DSS na iya gurfanar da Mahdi a kotu ranar Litinin ko wani lokaci nan kusa.
An riga an bayar da umarnin gurfanar da shi a gaban kotu. Bugu da ƙari, an umarci jami’an DSS da su tabbatar an kiyaye haƙƙin Mahdi yayin da yake tsare.
Mahdi Shehu ya kasance cikin ƙura saboda irin salon gwagwarmayarsa mai cike da ce-ce-ku-ce. Tun farkon shekarar 2024, an kama shi bayan ya yi kira ga Shugaba Bola Tinubu da ya binciki tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da manyan jami’an gwamnatinsa.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Abubakar Malami, tsohon Ministan Shari’a, ya bayyana dalilin kama Mahdi, sabanin ikirarin da lauyan ɗan gwagwarmayar ya yi a baya.
Lauyan Mahdi ya ce an kama shi ne saboda kiran da ya yi na a binciki tsohon Shugaba Buhari da wasu manyan jami’an tsohuwar gwamnatin.
Sai dai wata sanarwa daga lauyoyin Malami da A.A. Sherif ya sanya wa hannu ta ce an kama Mahdi ne bisa zargin karkatar da kuɗi.
Lauyoyin Malami sun rubuta cewa: “Mun samu labarin wata sanarwa ta manema labarai da aka fitar ranar 7 ga Fabrairu, 2024, da kuma ta watan Janairu 2024. A matsayinmu na lauyoyi ga Alhaji Abubakar Malami, SAN, da iyalansa, mun lura da matuƙar damuwa cewa wannan sanarwar ba ta daidai ba ce, tana ɓata suna, kuma tana ɗauke da bayanan ƙarya.
“Don haka, mun yanke shawarar yin wannan bayanin domin gyara abin da ya ɓaci don amfanin jama’a. Ba tare da ɓata binciken da ‘yan sanda ke yi ba, zargin ya shafi rubutaccen ƙorafi da muka gabatar ga Sufeto Janar na ‘Yan Sanda kan zargin karkatar da kuɗi...”