.....kantin sauki yana tashin farashin kayan abinci.
Muazu Hassan @ Katsina times
Jaridun Katsina times sun bi wasu manyan shagunan dake sayar da kayan masarufi a kwaryar birnin katsina da kewaye. Inda suka gano farashin kayan masarufi wadanda ake sayarwa a gwangwani,kwalaye,da kuma buhunna irin su dangin shinkafa da lemukan sha har da ruwan roba.
Abin da kewayen nasu ya gano,Kusan duk Manyan kantuna da shuganan da muka je,kudin kayan ,sukan kama kusan daya ķo kuma da bambanci dan kadan.
Babban inda muka samu bambanci shine Babban ķantin Al musik dake kusa da gadar kofar kaura, wanda aka Bude shi kwanan nan, sai kuma Al Musik dake bakin kasuwa titin kwauron dorowa.
A wàdannan kantuna biyu mun samu farashin kayan su, baki daya, suna sayar da kwara daya har zuwa adadin da kake bukata,dai dai da farashin sari.
Dukkanin kayan da ake sayarwa daya, daya, ana sayar dashi, kamar na mai sari ne, watau wanda zai saya, ya sayar yaci riba.
Wannan yà sanya farashin kantunan Al Musik, ya fi na kowa sauki, a shaguna da kantunan da wakilan mu suka zagaya cikin katsina.
Wani lamari kuma da muķa gano shine: Shagunan kantin sauki da gwamnatin Katsina ta bude wadanda, ma aikata kan iya zuwa su sayi abinci, kai tsaye cikin albashin su, cikin rahusa da ragowa,wannan shirin ya hana farashin kaya tashi ya kuma karya alkadarin masu bada bashin abinci da ruwa.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com