RUDANI: Mutane da dama sun mutu a Okija yayin turereniya a wurin rabon shinkafa a Jihar Anambra
- Katsina City News
- 21 Dec, 2024
- 58
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Lamarin ya faru ne a ranar Asabar 21 ga watan Disamba a dalilin cunkoson jama’a wajen karɓar shinkafa kyauta da ake rabawa mazauna yankin.
A wani bidiyo da Arinzechukwu Nwanonenyi ya wallafa a Facebook, wanda SaharaReporters ta samu, wani shaida ya bayyana alhinin da ke tattare da abin da ya faru a Okija cikin Anambra ta Kudu, inda aka ce turereniyar ta yi sanadin mutuwar mata da dama.
Bayanai sun nuna cewa mata da dama sun taru domin karɓar shinkafa da ake rabawa kyauta ta hannun Obijackson.
“Ina jin tausayin wannan lamari. Talauci abu ne mai muni. Da ace waɗannan matan da suka rasa rayukansu ba talakawa ba ne, ba za su kasance a wurin ba. Allah ya ji kansu, ya sa sun huta Amin,” in ji Nwanonenyi.
Sai dai, hukumomi ba su tabbatar da adadin mutanen da suka mutu ba tukuna.
Wannan al’amari ya nuna mawuyacin halin tattalin arzikin da mutane da dama ke ciki a wasu jihohin Najeriya.
SaharaReporters ta ruwaito a baya cewa wata irin wannan turereniya ta auku a makarantar Islamic High School da ke Bashorun, Ibadan, a safiyar Laraba, yayin taron bukukuwan Kirsimeti na yara, inda hakan ya yi sanadin mutuwar yara 35.
Taron wanda tashar rediyon Agidigbo 88.7 FM, Ibadan ta shirya, ƙarƙashin jagorancin Oriyomi Hamzat, tare da haɗin gwiwar Queen Naomi Silekunola Ogunwusi, tsohuwar matar Ooni na Ife. Ya taro cunkoson Talakawa mabukata don amsar shnkafar bikin Kirsimeti.
Shaidu sun bayyana cewa yara da dama sun fuskanci turereniya yayin tashin hankali, inda wasu suka jikkata kuma suke samun kulawa a asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan (UCH).