Arangamar Barayin Daji A Katsina: Manyan 'Yan Bindiga Sun Bakuncin Lahira
- Katsina City News
- 19 Dec, 2024
- 145
Katsina Times
A ranar, Litinin 17 ga Disamba 2024, an gudanar da wani taron addu'o,i a garuruwan Dutsinma, Tsaskiya, Zakka, Ummadau, da wasu sauran yankuna. Al’ummar yankin sun yi ta rokon Allah da ya kawo karshen matsalolin da suka addabi yankin, musamman hare-haren barayin daji. Alhamdulillah, addu'o’in sun samu karbuwa kamar yadda rahoton yau ya tabbatar.
Da safiyar ranar Talata 18 ga Disamba, da misalin karfe 5:58 na safe, an samu rahoton harin barayin daji a yankin Ummadau. Wadannan barayi sun fuskanci gagarumin fadan da abokan gabarsu, wanda hakan ya janyo asarar rayuka da dukiyoyi a tsakanin su.
Fadan ya barke ne tsakanin barayin daji da 'yan dabar Usman Modi-Modi, da aka fi sani da “’Yan Kambari.” Harin ya kai ga gidan Harisu, inda aka tabbatar da kashe shugabanni da manyan barayin da suka shahara wajen aikata miyagun laifuka.
Jaridun Katsina Times sun samu tabbacin kashe, Nasiru Bosho: Wannan fitaccen shugaban 'yan ta’adda, wanda ya ke da alhakin kula da dukkan makaman Usman Modi-Modi da shanunsa, an tabbatar da kashe shi a fadan. Nasiru shi ne shugaban sansanin Dogon Marke, wanda ya addabi yankin tsawon shekaru. Bala Yatsa: Wani babban dan dabar Usman Modi-Modi, shi ma ya rasa ransa a wannan rikici. Bala Yatsa ne ya kashe Modi-Modi a watannin baya, kuma wannan ya janyo takaddama mai tsanani a tsakanin 'yan ta’addan. Audu Mankare: Duk da cewa ya zuwa hada wannan rahoton mun samu labarin cewa bai cika ba yana numfashi, an harbe shi da harsashi wanda ya huda kirjinsa ta fito ta baya. Ana sa ran halin da yake ciki ba zai jure ba.
A yayin wannan fadan, an kwato shanu masu yawa da suka kasance mallakin Harisu. Wannan nasara ta dawo da martabar mutanen da suka sha fama da asarar shanu da barayin ke kwacewa a yankin.
Barayin sun yi gargadi ga mazauna kauyukan Kwayawa da Yar Kwana da su zauna cikin gidajensu, domin duk wanda ya fito zai iya fuskantar hadari. Wannan rikici ya nuna cewa yanzu barayi sun fara fada da kansu, lamarin da ya rage tsoratarwa ga al’umma.