Bello Turji Ya Yi Barazanar Kai Munanan Hare-hare, Saboda Kama Abokinsa, Wurgi
- Katsina City News
- 16 Dec, 2024
- 262
Katsina Times
Shahararren dan ta’adda, Bello Turji, ya bayyana barazanar tada Hankali ta Hanyar Kai hare-hare bayan kama abokinsa na kut-da-kut, Wurgi, wanda ke daya daga cikin manyan masu taimaka masa wajen tattaunawa da karbar kudin fansa daga mutanen da suka sace a yankin gabashin jihohin Sokoto da Zamfara.
Rahotanni daga majiyoyin tsaro sun bayyana cewa, kama Wurgi ya harzuka Turji matuka, lamarin da ya sanya fargaba a zukatan mazauna yankunan da abin ya shafa tare da hukumomin tsaro.
Wata majiya mai tushe ta shaida wa Zagazola Makama cewa, Bello Turji ya riga ya tuntubi wasu fitattun shugabanni a yankin Shinkafi, ciki har da dagatai da sarakunan gargajiya, yana barazanar kai hare-hare kan al’ummominsu domin tabbatar da cewa an saki Wurgi daga hannun jami’an tsaro.
Baya ga haka, rahotanni sun ce Turji ya yi alkawarin kashe dukiya mai yawa, ko dabbobi, don ganin an saki Wurgi. Ya bayyana cewa yana da adadi mai yawa na mutane da dabbobi karkashin ikon sa, kuma ya bayyana shirinsa na amfani da su wajen matsa wa hukumomi lamba.
Idan kuwa hakan ya ci tura, Turji ya yi barazanar tada hankali a dukkan yankin gabashin Sokoto da Shinkafi, tare da yin barna mai tsanani a wuraren da abin ya shafa. Har ila yau, ya yi barazanar kashe wasu daga cikin mutanen da suke hannunsa, wadanda suka hada da mazauna yankunan Isa, Sabon Birni, da Shinkafi.
Wannan ba shi ne karon farko da Turji ke amfani da irin wannan salo ba. Shekaru biyar da suka gabata, ya yi irin wannan barazana har sai da aka saki wani abokinsa mai suna Dikko Chida. A lokacin, Turji ya gargadi gwamnati kan mummunan abin da zai faru, wanda hakan ya tilasta wa gwamnati yin sulhu tare da sakin Dikko.
Kama Wurgi wata dama ce ga hukumomi don kawo wa ayyukan Turji cikas. Sai dai, yadda gwamnati za ta tafiyar da lamarin yanzu zai tantance ko barazanar Turji za ta tabbata ko kuma za a samu mafita mai dorewa ga matsalar ‘yan ta’adda a yankin.