Tsohon Dan takarar Gwamnan jihar Katsina a jam'iyyar PDP ya raba Miliyoyin Kudi ga tsaffin 'Yan takara na jam'iyyar a fadin jihar

top-news


Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times

Tsohon Dan takarar Gwamnan jihar Katsina Sanata Yakubu Lado Danmarke na Jam'iyyar PDP a jihar Katsina ya raba Miliyoyin Kudi ga 'Ya'yan Jam'iyyar PDP da 'Yan takarar a fadin jihar Katsina.

Tsohon Dan takarar bisa wakilcin Hon. Alhaji Haruna Jani, da Hon. Nura Amadi Kurfi, tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP Hon. Magaji Danɓachi, da Shugaban Jam'iyyar PDP na Riƙon ƙwarya Alhaji Musa Abdulkarim suka jagoranta.

Da yake gabatar da jawabin sa a madadin tsohon Dan takarar Gwamnan jihar Katsina Sanata Yakubu Lado Danmarke, Honorable Alhaji Haruna Jani ya bayyana fatan Alheri ga Dukkanin 'yan takarar da 'ya'yan Jam'iyyar PDP a fadin jihar Katsina. Ya kara da cewa, "Sanata Yakubu Lado Danmarke ya Umarce ni da na bayyana jadawalin yanda rabon kudin buda baki da zai baku a watan Ramadana na wannan shekara zai kasance" yace  a bawa tsohon Ciyaman na PDP da aka kwacewa kujera a 2022 tsabar kudi Naira dubu 50, Mataimakinsa Naira dubu 30, Kansilolin jihar Katsina guda 361 za'abasu ko wanne Naira dubu 30, 'Yan takarar majalisar Dokokin jihar Katsina na PDP su 34 da sukayi takara a a tsakanin 2019 da 2023  karkashin jam'iyyar PDP suma am basu ko wanne dubu 100, sai kuma wadanda suka yi takarar Majalisar Tarayya ta Abuja a jihar Katsina su goma sha biyar dukkanin su Sanata ya bada Naira dubu 200 a bawa ko wannensu. Inji Honorable Jani. A karshe ya gidewa Sanata Yakubu Lado bisa ga irin wannan gagarumar gudummawa da ya ke bawa jam'iyyar PDP tsawon shekaru.

Tun da farko tsohon Shugaban Jam'iyyar PDP na jihar Katsina, Alhaji Magaji Danɓachi ya bayyana irin wannan gudumawa da Sanata Yakubu Lado ke bayarwa a matsayin Ruhin Jam'iyyar PDP, yace idan har wani yana jin cewa shi dan PDP ne na hakika shima yayi irin yanda sanata Yakubu Lado Danmarke yake yi. Yace "Don haka duk wanda baya tare da Yakubu Lado Danmarke ko dan gidan mu ne bama tare da shi, wanda yake tare da Sanata Yakubu Lado muma muna tare da shi," yace kuma da yardar Allah, Yakubu Lado sai ya zama Gwamna a jihar Katsina. 

Taron ya gudana a babban dakin taro na shelkwatar jam'iyyar PDP a jihar Katsina dake bisa titin zuwa kano a ranar Lahadi 31 ga watan Maris.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

isahsani4031@gmail.com

Congratulations