Dakta Ibrahim Iyal Gafai Ya Zama Mataimakin Shugaban Hukumar Hisbah a Katsina
- Katsina City News
- 24 Dec, 2024
- 114
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Dakta Ibrahim Iyal Gafai ya zama Mataimakin Shugaban Hukumar Hisbah na jihar Katsina, bayan wani nazari na cancanta da shugaban hukumar, Dakta Aminu Usman Abu Ammar, ya jagoranta. Wannan sanarwa ta fito ne daga bakin Dakta Aminu Usman a wata hira da ya yi da jaridar Katsina Times a ranar Talata.
A cewarsa, an zabi Dakta Ibrahim Iyal Gafai, wanda yake daga Darikar Tijjaniyya, bisa duba cancanta da hangen nesa na tabbatar da hadin kai tsakanin al'ummomin musulmi a jihar. Ya ce, “Mun zabi wannan matashi jajirtacce domin kara karfafa hukumar Hisbah ta samu ci gaba da gudanar da ayyukanta cikin nasara.”
Dakta Aminu ya kuma yi karin haske kan tsarin hukumar, yana cewa ta tattaro mambobi daga bangarori daban-daban na addinin musulunci. “A hukumar Hisbah muna da wakilai daga kowanne bangare, ciki har da ‘Yan Shi’a, Darika, Izala, da Kur’aniyyun. Wannan tsarin ya tabbatar da cewa Hisbah tana wakiltar dukkan al’ummar jihar Katsina,” in ji shi.
Ya kuma bayyana cewa an dauki matasa fiye da 300 daga kananan hukumomi 34 na jihar Katsina domin basu horo a ofisoshin jami’an tsaron Civil Defence. Dakta Aminu ya ce, “Mun tabbatar da cewa an samu wakilcin matasa daga dukkan bangarorin don tabbatar da aikin hukumar yana tafiya daidai.”
A nasa jawabin, Dakta Ibrahim Iyal Gafai ya nuna godiya ga Dakta Aminu Usman bisa wannan dama da aka ba shi. Ya bayyana mukamin a matsayin wata dama ta yin hidima ga al’ummar jihar Katsina, musamman ta fuskar inganta rayuwar ma’aurata da al’umma baki daya.
Dakta Ibrahim ya sha alwashin gudanar da aikinsa cikin gaskiya, rikon amana, da hadin kai domin kawo sauyi mai ma’ana ga jihar.
A yayin da yake mika takardar amincewa ga mukamin da aka bashi, Dakta Ibrahim ya samu rakiyar ‘yan uwa, abokan arziki, da shugabannin unguwanni daga yankinsa. Sun bayyana farin cikinsu da godiya bisa wannan ci gaba da ya samu, tare da fatan alheri gare shi a sabuwar amanarsa.