Taron KCF na Shekarar 2024: Zai mayar da Hankali Kan Yaki da Talauci da Tsaro a Katsina
- Katsina City News
- 25 Dec, 2024
- 27
Zaharaddeen Ishaq Abubakar, Katsina Times
Shugaban Kungiyar KCF jihar Katsina, Alhaji Aminu Abubakar Danmusa
Kungiyar Tattaunawa ta Katsina, "Katsina Consultative Forum" (KCF) ta shirya gudanar da babban taron shekara-shekara na 2024 wanda zai gudana a ranar 29 ga Disamba, a babban dakin taro na masaukin shugaban kasa, Banquet Hall, a gidan gwamnatin jihar Katsina. Wannan na zuwa ne bayan da shugaban kungiyar, Alhaji Aminu Abubakar Danmusa, ya sanar wa manema labarai a Abba Saude House ranar Alhamis, 25 ga Disamba.
Taron ya mayar da hankali kan yaki da talauci, tsaro, da kuma tabbatar da ci gaban dawwama a jihar Katsina. Shugaban kungiyar ya bayyana cewa, wannan babban taron zai zama wata kafa ta musamman don tattaunawa da yin duba kan manyan matsalolin da ke addabar jihar, tare da zakulo hanyoyin samar da mafita masu dorewa.
Taron zai tara kwararru, ‘yan siyasa, shugabannin al’umma, da wakilai daga kungiyoyi masu zaman kansu don samar da mafita ga kalubalen jihar. Alhaji Danmusa ya bayyana cewa, bayan taron, za a samar da bayani mai dauke da shawarwari masu amfani da za a raba wa masu ruwa da tsaki domin tabbatar da aiwatar da dabarun ci gaba.
Muhimman Matsalolin Da Za a Tattauna
Rahoton Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ya nuna cewa jihar Katsina na cikin yankunan da talauci ya fi kamari, inda alkaluman shekarar 2020 suka nuna kashi 74.1% na al’ummar jihar na fama da talauci. Wannan matsalar ita ce tushen yawancin matsalolin tsaro da sauran kalubale a al’umma.
Ana samun karuwar shaye-shaye a tsakanin matasa, lamarin da ke barazana ga makomar jihar. A cikin jawabinsa ga manema labarai Danmusa ya bayyana wasu muhimman Ayyuka da KCF ta gudanar a shekarar 2024 domin yakar matsalolin da ke damun jihar. Wadannan ayyuka sun hada da:
Shirya taruka da shirye-shiryen wayar da kai kan illar shaye-shaye a kafafen yada labarai kamar Alfijir FM da Radio Nigeria Kaduna.
Wayar da kan shugabannin al’umma don fadakar da matasa a kananan hukumomi 34 na jihar.
Shirya tarukan tattaunawa da masu ruwa da tsaki don samar da dabarun yaki da shaye-shaye.
Samar da ruwan sha ga gidajen kwanan NDLEA a Katsina, da kuma shirye-shiryen gina cibiyar gyaran hali domin tallafa wa masu shaye-shaye su dawo cikin al’umma.
Alhaji Danmusa ya jaddada bukatar hadin kai tsakanin gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu, da al’umma wajen ganin an cimma burin kawo karshen talauci da matsalolin tsaro a jihar Katsina.
Wannan taron na 2024 zai kasance babbar dama ta zakulo sabbin hanyoyin warware matsalolin jihar Katsina da kuma tabbatar da jin dadin al’umma baki daya.