BARAYIN DAJI SUN BUDE WUTA A GARIN MARA TA DANMUSA.
- Katsina City News
- 26 Aug, 2023
- 695
@ Katsina Times.
A ranar jumma a 24/8/2023,da misalin karfe uku na Rana wasu yan bindiga sukayi shigar burtu suka je bakin tashar garin Marar zamfarawa dake karamar hukumar Danmusa.
Bayan yan bindigar sun isa wajen, kowannen su ya samu wuri ya tsaya kamar fim.
Sannan suka fito da bindigogi suka fara ruwan wuta,bayan sun zubar da harsashin da suka zo dashi .
Yan bindigar sun hau baburansu suka koma inda suka fito.
Ganau sun fada ma katsina times cewa an kashe mutane biyu an jikkakata wasu da yawan gaske a wannan harin.
Wani abin takaici,wadanda aka jikkatan a harin, da aka kaisu asibitin, garin Danmusa sai da suka biya kudin magani da nayi masu aiki kafin a kula su.
Dan uwan Wanda aka jikkata ya fada ma katsina times cewa, asibitin sun ki taba masu raunin harbin har sai da suka Nemo kudi magani da aiki suka bayar.
Masu raunin an kawo su asibiti a katsina domin Karin magani da kulawa.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Jaridar taskar labarai
@ www.jaridartaskarlabarai
07043777779 08057777762