AN ƊAURA AUREN ƊIYAR HON.MAJIGIRI A GARIN MASHI

top-news



Yau 08/09/2023.

An ɗaura auren Ɗiyar Zaɓaɓɓen Ɗan majalisar tarayya mai wakiltar kananan hukumomin Mashi da Dutsi Hon. Salisu Yusuf Majigiri (Garkuwan Gabas Katsina)

An ɗaura auren Khadija Salisu Majigiri da  Angonta Arc. Muhammad Adamu Ɗoguru a Babban masallacin juma'a na ke garin Mashi.

Ɗaurin auren ya samu halartar Manyan Manyan baƙi na ciki da wajen jahar nan, akwai manyan yan siyasa,Sarakai,Attajira,Malamai,Yan kasuwa,Yan boko da sauran su 

Gwamnan jihar Katsina Malam Dikko Umar Raɗɗa PhD shi ne Waliyin Amarya wanda ya bada auren. 

Akwai Masoya da magoya baya daga Sassa daban-daban wadanda suka samu shaidar wannan ɗaurin aure mai albarka.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *