Gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda ya halarci taron Sanin Makamar Aiki da raya ƙasa a Rwanda

top-news

Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya halarci taron sanin makamar aiki da shirin raya kasashe na majalisar dinkin duniya ya shirya a kasar Rwanda

Gwamnan jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, PhD, tare da takwarorinsa gwamnonin Nijeriya ya samu halartar taron kara gogewa da sanin makamar aiki da kungiyar gwamnonin kasar hadin guiwa da shirin raya kasashe na majalisar dinkin duniya UNDP ya shirya a birnin Kigali na kasar Rwanda.

Horarwar za ta ba jami'an gwamnati damar samun alaka kyakkyawa tsakanin bangaren gwamnati da na masu zaman kansu, lalubo sabbin hanyoyi da dabarun zuba jari don tattalin arziki ya bunkasa da dorewar cigaba.

Wannan taron sanin makamar aiki ya zo daidai da kudirin Malam Dikko Umaru Radda na zakulo hanyoyin mabambanta da za su sa tattalin arzikin jihar Katsina ya yi ingancin da duk wani Bakatsine zai amfana.

Shirin raya kasashe na majalisar dinkin duniya UNDP hadin guiwa da kungiyar gwamnonin Nijeriya NGF ne suka shirya taron, domin horar da gwamnonin hanyoyi da dabaru salon mulki ta yadda za su rika jagorancin al'umma yadda ya dace.

Taron na gudana ne daga ranakun 24-27 ga watan Agusta, 2023.

SSA Isah Miqdad,
25/8/2023.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *