Za A Mayar da Wutar Lantarki A Arewa Cikin Kwanaki Biyar - Gwamnatin Tarayya
- Katsina City News
- 29 Oct, 2024
- 140
Ministan Wuta, Mista Adebayo Adelabu, ya tabbatar da cewa a cikin kwanaki biyar masu zuwa za a dawo da wutar lantarki a jihohin arewa 17 da ke fama da matsalar hasken wuta sakamakon lalata layin wutar Shiroro-Kaduna.
Ministan ya bayyana hakan a ranar Litinin yayin da yake yi wa manema labarai bayani a Fadar Shugaban Kasa bayan ganawa da Shugaba Bola Tinubu.
A cewarsa, za a gyara layin da aka lalata cikin kwanaki uku zuwa biyar.
Ya kara da cewa, shugaba ya riga ya umarci mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro da kuma shugabannin hukumomin tsaro da su samar da tsaro ga wadanda za su gyara layin da aka lalata.
Ministan ya tabbatar da cewa, da tsaron da za a samar, ma’aikatan Kamfanin Wutar Lantarki na Najeriya (TCN) tare da ‘yan kwangila za su samu kwarin gwiwar komawa bakin aiki don gyara layin.
“Ina roƙon ‘yan uwanmu na arewa da su yi hakuri, nan ba da dadewa ba za a dawo da wuta. Kuma dole mu haɗa kai domin kare grid ɗin mu na ƙasa daga sake lalatawa,” inji ministan.