Dakta Bashir Kurfi Ya Bar Kotu Zuwa Gidansa

@ Katsina TimesJaridun Katsina Times sun tabbatar da cewa Dakta Bashir Kurfi ya cika dukkan sharuɗɗan da kotu ta gindaya masa, kuma an sallame shi.Bayan fitowarsa daga kotu, Dakta Kurfi…

Katsina City News July 13, 2026  ·  12:00 AM
| 157 Views
Dakta Bashir Kurfi Ya Bar Kotu Zuwa Gidansa
Dakta Bashir Kurfi Ya Bar Kotu Zuwa Gidansa

@ Katsina Times

Jaridun Katsina Times sun tabbatar da cewa Dakta Bashir Kurfi ya cika dukkan sharuɗɗan da kotu ta gindaya masa, kuma an sallame shi.


Bayan fitowarsa daga kotu, Dakta Kurfi ya fara komawa hedikwatar ’yan sanda domin karɓar kayansa da ke hannunsu.


Katsina Times ta kuma samu labarin cewa zai fara ganawa da likitocinsa, sannan zai kwana guda a Katsina kafin daga bisani ya koma Zariya, inda iyalansa suke.

Advertisement

BSIL Security Report


Sakinsa ya samu jinjina da yabo daga jama’a da kuma sauran ’yan gwagwarmaya da suka halarci kotun domin nuna masa goyon baya da tausayawa.


An gayyaci Dakta Kurfi a ranar Larabar da ta gabata, sannan aka gurfanar da shi a gaban kotu a ranar Alhamis. A wancan lokacin, kotun ta bayar da umarnin a ci gaba da tsare shi domin kammala bincike.


Har ila yau, jaridun Katsina Times sun samu tabbacin cewa wasu manyan mutane daga sassa daban-daban na ƙasar nan sun shiga cikin lamarin, kuma gwamnatin Jihar Katsina ta saurari buƙatunsu.

Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 6 + 6?