Sabon Labari Kan Tsare Dakta Bashir Kurfi: Ya Bayar da Rubutaccen Bayani ga 'Yan Sanda

Daga Mu'azu Hassan@ Katsina TimesJaridar Katsina Times ta samu tabbacin cewa Dakta Bashir Kurfi, wanda ke tsare a hannun 'yan sanda bisa umarnin kotu, ya rubuta bayaninsa ga jami'an bincike…

Katsina City News July 10, 2026  ·  12:00 AM
| 37 Views
Sabon Labari Kan Tsare Dakta Bashir Kurfi: Ya Bayar da Rubutaccen Bayani ga 'Yan Sanda
Sabon Labari Kan Tsare Dakta Bashir Kurfi: Ya Bayar da Rubutaccen Bayani ga 'Yan Sanda

Daga Mu'azu Hassan@ Katsina Times

Jaridar Katsina Times ta samu tabbacin cewa Dakta Bashir Kurfi, wanda ke tsare a hannun 'yan sanda bisa umarnin kotu, ya rubuta bayaninsa ga jami'an bincike a gaban lauyansa.


Majiyoyi sun bayyana cewa bayan kammala rubuta bayanin, lauyansa ya karanta shi tare da tabbatar da cewa babu wata magana da ke cikinsa da za ta iya cutar da wanda yake karewa.


A cikin bayanin nasa, Dakta Bashir Kurfi ya jaddada cewa bai taba cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta biya wa 'yan bindiga kuɗin aikin Hajji ba. Ya ce abin da ya bayyana a hirar da ya yi shi ne cewa akwai zarge-zarge da ake yi, kuma ya kara da cewa idan har akwai irin waɗannan zarge-zarge, ya rage wa gwamnati ta fito ta yi wa jama'a cikakken bayani domin kawar da shakku.


Advertisement

BSIL Security Report

Binciken da Katsina Times ta gudanar ya nuna cewa 'yan sanda sun kammala bincikensu tare da tattara shaidu da suke shirin gabatarwa a gaban kotu.


Har ila yau, binciken ya gano cewa lauyoyin Dakta Bashir Kurfi sun sake gabatar da sabon buƙatar beli a rubuce gaban kotu, bayan da tun farko suka nemi a ba shi belin da baki a zaman kotun da ya gabata.


Ana sa ran za a ci gaba da sauraron shari'ar a ranar Litinin, 14 ga watan Yuli.


Written by

Katsina City News

Katsina City News is a journalist and correspondent at Katsina Times — covering local, national and international news with a focus on Northern Nigeria.

Comments (0)

No comments yet. Be the first to share your thoughts!

Leave a Comment

What is 1 + 5?