MAJALISAR DINKIN DUNIYA TA KOKA A KAN BAZUWAR MAKAMAN LIBYA A NAJERIYA

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes05062026_073859_Screenshot_20260605-083749.jpg

Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi 

Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana cewa makaman da a ka wawashe a lokacin rikicin Libya a shekara ta 2011, sun kare a hannun Yan ta'adda da ma su tayar da kayar-baya a Najeriya.

Wannan tsokaci na zuwa ne daga Wakiliyar Majalisar Dinkin Duniya ta fannin Rage Bazuwar Makamai, Izumi Nakamitsu, a lokacin da ta ke wani jawabi ga wakilai a hedikwatar majalisar da ke birnin New York na kasar Amurka.

Ta yi tsokacin ne a yayin tattaunawa a kan batun yaduwar haramtattun makamai a duniya da tasirin su a kan zaman lafiya da tsaro.

Wakiliyar ta bayyana jimamin cewa makaman da su ka bazu a lokacin rigingimu na jawo cigaban tashe-tashen hankula ko bayan rigingimun farko sun wuce, Wanda ke kara iza wutar rashin zaman lafiya da ta'addanci a tsakanin kasashe.

Kamar yadda ta bayyana, makaman da a ka sace a lokacin rikicin da ya kifar da gwamnatin Shugaban Libya Muammar Gaddafi, sun sake bayyana a yankunan Sahel, ciki kuwa har da Najeriya.

Ta lura da cewa daga bisani an gano wasu daga cikin makaman a hannun ma su tayar da kayar-baya a yankin, Wanda hakan ke nuni da yadda makamai da su ka fito daga wani rikici ke bayar da gudummuwa wajen samun tashe-tashen hankula a wasu wuraren nesa da gidan su na ainihi.

Follow Us