Muazu Hassan @ Katsina Times
Alkalin Babbar Kotun Tarayya ta 1 da ke jihar Katsina, Mai Shari’a Aminu B. Aliyu, ya saka ranar Juma’a, 27 ga watan Nuwamba, domin sauraren karar da jam’iyyar APC ta jihar Katsina ta shigar a kan wasu da suka samu takara a wasu jam’iyyun.
APC ta kai karar ne bisa hujjar cewa waɗanda aka ba tikitin takara, waɗanda suka fito daga cikin jam’iyyun PDP, ADC da APM, ba su cancanci tsayawa takara ba bisa wasu ƙa’idojin da dokar zaɓe ta tanada ta shekarar 2027.
Hujjojin sun haɗa da cewa waɗanda suka samu tikitin takarar sun same su ne bayan wa’adin da hukumar zaɓe ta bayar na gabatar da sunayen dukkan ’yan jam iyya ya ƙare.
Haka kuma, ba za ka iya tsayawa takara ba sai kana ɗan jam’iyya, sannan sunanka yana cikin kundin sunayen ’yan jam’iyyar da ke rumbun adana bayanai na hukumar zaɓe.
Biyu daga cikin waɗanda shari’ar ta shafa sun bayyana wa jaridun Katsina Times cewa lamarin ya zo musu da mamaki, amma sun shirya tunkararsa.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page; katsina city news
Facebook group. Katsina city news
Facebook page. Jaridar taskar labarai
All social media handles @ katsina times
07043777779


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!