Mu'azu Hassan @ Katsina Times
Binciken da Jaridun Katsina Times suka gudanar ya nuna cewa har yanzu Alhaji Lawal Musa Daura bai fito a hukumance ya bayyana matsayarsa kan makomar siyasarsa ba.
Sai dai majiyoyi daban-daban sun tabbatar wa Katsina Times cewa bai amince da tayin takarar Sanata da aka yi masa a jam'iyyar ADC ba. Haka kuma, an ruwaito cewa jam'iyyar ADC ta riga ta tsayar da wani ɗan takara domin wakiltarta a Yankin Sanatan Daura.
Majiyoyin sun kuma bayyana cewa Lawal Musa Daura zai gana da magoya bayansa ranar Lahadi mai zuwa a wani ɗakin taro da ke birnin Katsina, inda ake sa ran zai bayyana matsayarsa kan takararsa.
A cewar majiyoyin, akwai yiwuwar Lawal Musa Daura ya koma jam'iyyar APM, wadda wasu jiga-jigan PDP suka koma domin gujewa rikice-rikicen da ke addabar jam'iyyar PDP.
Haka kuma, majiyoyin sun ce idan babu wani sauyi na ƙarshe, ana sa ran Lawal Musa Daura zai kasance mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar APM, wanda ake zargin Gwamnan Jihar Oyo, Seyi Makinde, zai jagoranta a zaɓen shekarar 2027.
Hakazalika, majiyoyin sun ce akwai yiwuwar Dakta Mustapha Inuwa shi ma ya koma jam'iyyar APM domin neman takarar gwamnan Jihar Katsina, tare da mabiyansa su ma su fafata a ƙarƙashin jam'iyyar.
Idan ba a samu wani sauyin matsaya ba, ana sa ran cikin kwanaki kaɗan masu zuwa za a ayyana Dakta Mustapha Inuwa a matsayin ɗan takarar gwamnan jam'iyyar APM.
Majiyoyin sun kuma ce har ma ɓangaren jam'iyyar PDP na Tanimu Turaki na nazarin yiwuwar ƙulla ƙawance da jam'iyyar APM domin samar wa 'yan takararsu da magoya bayansu mafita.
Sai dai duk waɗannan bayanai sun samo asali ne daga majiyoyi, kuma ana sa ran komai zai fito fili cikin kwanaki kaɗan masu zuwa, lokacin da za a bayyana matsayoyin hukumance.
Katsina times: @ www.katsinatimes.com
Facebook page; katsina city news
Facebook page .jaridar taskar labarai
All social media handles. @ katsina times
07043777779


Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!