Daga Mu'azu Hassan@ Katsina Times
Jaridar Katsina Times ta samu tabbacin cewa Dakta Bashir Kurfi, wanda ke tsare a hannun 'yan sanda bisa umarnin kotu, ya rubuta bayaninsa ga jami'an bincike a gaban lauyansa.
Majiyoyi sun bayyana cewa bayan kammala rubuta bayanin, lauyansa ya karanta shi tare da tabbatar da cewa babu wata magana da ke cikinsa da za ta iya cutar da wanda yake karewa.
A cikin bayanin nasa, Dakta Bashir Kurfi ya jaddada cewa bai taba cewa Gwamnatin Jihar Katsina ta biya wa 'yan bindiga kuɗin aikin Hajji ba. Ya ce abin da ya bayyana a hirar da ya yi shi ne cewa akwai zarge-zarge da ake yi, kuma ya kara da cewa idan har akwai irin waɗannan zarge-zarge, ya rage wa gwamnati ta fito ta yi wa jama'a cikakken bayani domin kawar da shakku.
Binciken da Katsina Times ta gudanar ya nuna cewa 'yan sanda sun kammala bincikensu tare da tattara shaidu da suke shirin gabatarwa a gaban kotu.
Har ila yau, binciken ya gano cewa lauyoyin Dakta Bashir Kurfi sun sake gabatar da sabon buƙatar beli a rubuce gaban kotu, bayan da tun farko suka nemi a ba shi belin da baki a zaman kotun da ya gabata.
Ana sa ran za a ci gaba da sauraron shari'ar a ranar Litinin, 14 ga watan Yuli.



Comments (0)
No comments yet. Be the first to share your thoughts!