Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi
Tsohon Mataimakin Director a hukumar Yansandan Ciki (DSS), Dennis Amachree ya bayyana cewa bugawar zuciya ne sanadin rasuwar tsohon shugaban mulkin soja Janar Sani Abacha, ba wai guba ba kamar yadda a ke yadawa.
Dennis Amachree ya ce mafi yawan rahotannin da a ke bazawa dangane da musababbin rasuwar tsohon shugaban Kasar na mulkin soja, jita-jita ce da labarun kanzon kurege.
Tsohon Jami'in Tsaron ya bayyana cewa dukkanin sakamakon bincike da a ka gudanar, ya tabbatar da cewa bugawar zuciya ne sanadiyyar rasuwar Abacha, sabanin maganganun da ke yaduwa bakunan mutane.
Dennis Amachree dai ya bayyana hakan ne a wani bangare na littafin da ya wallafa, da Kuma hirar da a ka yi da shi a tashar talbijin ta TVC.