HUKUMAR IMF TA CE KARIN YAN NAJERIYA MILIYAN 60 SUN SHIGA TALAUCI

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes11062026_175210_Imf2.jpg



Daga Garba Abu Abdullahi Jikamshi 

Hukumar bayar da tallafi ta Kasa da Kasa wato IMF ta bayyana cewa karin Yan Najeriya miliyan 60 sun shiga yanayi na kangin talauci.


Hukumar ta ce matakan da shugaba Tinubu ya aiwatar a cikin shekaru uku, da su ka hada da cire tallafin man fetur da sakin hada-hadar chanjin kudade, sun taimakawa kasar matuka, to amma an samu karin mutane da su ka shiga halin talauci.


A yayin da Masana Tattalin Arziki ke yabawa da wadannan matakai, kusan kashi 63 cikin dari na mutanen kasar sun shiga tasku na talauci, haka Kuma kusan kimanin mutane miliyan 27 ne ke fuskantar barazanar rasa samun abinda za su ci.


Hukumar ta IMF, a cikin wata sanarwa da su ka fidda, ta ce cigaba da matsalar tsaro a yankin Arewacin Najeriya da ke noma mafi akasarin abinda a ke ci a kasar, zai kara ta'azzara matsalolin tattalin arziki da wahalar rayuwa.


IMF ta yi gargadin cewa hauhawar farashin abinci da man fetur da takin zamani zai iya jefa talakawa cikin mawuyacin hali, zai Kuma samawa kasar kudaden shiga.

Follow Us