KatsinaTimes | 26 Nov 2025
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, Ph.D, ya rattaba hannu kan dokar kasafin kuɗin shekarar 2026 mai darajar N897.8bn, wanda hakan ya tabbatar da Katsina a matsayin jiha ta farko a Najeriya da ta kammala kasafin na shekarar 2026.
An gabatar da kudirin kasafin kuɗin ne ga Majalisar Dokoki kimanin kwanaki 21 da suka gabata, inda majalisar ta ce an yi aiki mai zurfi don tabbatar da cewa kudirin ya taru ne bisa muradun al’umma daga matakin ƙasa.
Yayin taron rattaba hannun, Kakakin Majalisar Dokoki ta Jihar Katsina, Rt. Hon. Nasir Yahya, ya bayyana cewa majalisar ta yi aiki tare da bangarori daban-daban domin tabbatar da cewa kasafin ya dace da bukatun jama’ar jihar.
Da yake jawabi, Gwamna Radda ya ce wannan shi ne karo na farko a tarihin jihar da fiye da kaso 80 cikin dari na kasafin kuɗi ya tafi kan manyan ayyuka, abin da ya ce ya nuna aniyar gwamnatinsa ta inganta ci gaban jama’a ta hanyar ayyuka masu dorewa.
Manyan Abubuwan Da Ke Cikin Kasafin 2026 sun hada da, Jigon kasafi: Building Your Future (III) Jimillar kasafi: N897.8bn Manyan ayyuka (Capital): N730.1bn (81.32%) Kuɗin gudanarwa (Recurrent): N167.7bn (18.68%)
Muhimman bangarori, Ilimi: N156.3bn
Ayyuka da gine-gine: N117.1bn, Noma: N78.6bn, Lafiya: N67.5bn, Ruwa: N62.8bn, Muhalli: N53.8bn.
Gwamnan jihar ya bayyana cewa kasafin ya samo asali ne daga tsarin shawarwarin jama’a, inda aka tattara ra’ayoyi daga mutane 71,384 ta wajen tarukan jin ra’ayi, tare da bayanai daga gidaje 6,649 a gundumomi 361 a kananan hukumomi 34.
Taron rattaba hannun ya samu halartar mambobin majalisar dokoki, ’yan majalisar zartarwa, Babban Mai Shari’a na jihar da sauran manyan jami’an gwamnati.