TARON TUNAWA DA MARIGAYI DAKTA YUSUFU BALA USMAN NA KWALEJIN BALA USMAN DAURA!!!.....YA BAR BAYA DA KURA!!!

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes22112025_201237_IMG-20251122-WA0142.jpg



Wakilan katsina times 
Anyi wani taro a kwalejin yusufu Bala usman dake garin Daura, jahar katsina, don tunawa da Marigayi yusufu Bala Usman( Allah ya jikanshi da Rahama)
Taron wanda kwaikwayo ne da irin wanda Makarantar kimmiya da fasaha ta katsina keyi domin tunawa da Hassan Usman katsina. Da kuma wadda Kwalejin Dutsinma keyi domin tunawa da Isah Kaita. 
Kwalejin ta Daura ta rubuta ma gwamnatin katsina domin bata tallafin shirya taron.wanda gwamnatin ta bayar da tallafin naira milyan biyar.
Anyi taron a ranar laraba 18 ga watan Nawumba a harabar Makarantar.hotuna da bidiyon da aka dora a shafin labarai na fasaha media stream, taron yafi kama da na wata kungiyar dalibai ta wani bangaren karatu ba taron tunawa da Babban Mutum kamar Marigayi yusufu Bala Usman ba.
Wasu Malamai  a Makarantar ta kwalejin yusufu Bala usman sun bayyana ma jaridun katsina times cewa ..sam taron ba ayi masa tsari mai kyau ba.

Sunyi zargin ba a gayyato masana da zasu tattauna waye yusufu Bala usman na da kuma irin koyarwar da ya bari.
Malaman sunyi ikirarin cewa, mun ga yadda akai taron tunawa da Hassan usman da kuma Isah kaita a  katsina da Dutsinma. Suka ce a Daura sam ba a dau ilmi ba.
Mahalarta taron sunyi korafin wadanda suke a dakin taron ba ruwa ba abinci,balle wani  minti na motsa baki.
Wasu Ma aikatan kwalejin sunyi zargin cewa, kudin da gwamnatin katsina ta bada bisa tsammanin kwalejin zata kara da na ta,tayi abin a yaba , ba a kashe su ba.
Sunyi ikirarin an bada gudummuwar Naira milyan biyar.amma a ina take har aka kashe ta a taron?
Jaridun katsina times sun tuntubi shugaban kwalejin akan zargin basu yi abin da ya dace ba, wajen kashe kudin da gwamnati ta basu don shirya taro mai kyau.
Shugaban kwalejin ya karyata duk zarge zargen, ya kuma ce mai kula da kudin kwalejin yayi mana bayanin yadda aka kashe kudin domin shirya taron.
Burser, na kwalejin yace kudin da gwamnatin katsina ta bada a asusun kwalejin aka ajiye su.kuma duk abin da za a kashe shine yake badasu.yace kwamitin taron sun tsara kashe Naira MIlyan uku da doriya a shirya taron .daga ciki akwai dubu dari tara na abincin da abin sha akwai na masu jawabi, akwai na "yan jaridu da "yan midiya,da sauran ayyukan taron yace dukkanin abinda aka tsara za a kashe ni na bada kudin .
Burser, ya kara da cewa akwai abin da ya rage acikin kudin, wanda akwai abin da aka tsara za ayi dasu wanda ya shafi taron bayan an kammala taron ,kamar rubuta takardar bayan taro da baiwa "yan jaridu don su buga.inji shi

Follow Us