PDP Ta Kori Wike, Anyanwu, Ajibade, Fayose Da Nwachukwu Kan Zargin Cin Amanar Jam’iyya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes15112025_174454_FB_IMG_1763228642129.jpg

Katsina Times 

Jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) ta sallami wasu manyan jiga-jiganta da suka hada da Nyesom Wike, Sanata Samuel Anyanwu, Kamaldeen Ajibade (SAN), tsohon Gwamna Ayo Fayose da Hon. Austin Nwachukwu, bisa zargin aikata ayyukan cin amanar jam’iyya.

Korafin ya fito ne daga babban taron gangamin jam’iyyar na shekarar 2025 da ake gudanarwa a Ibadan, inda wakilai suka kada kuri’ar amincewa da hukuncin cikin rinjaye.

PDP ta ce matakin na daga cikin dabarunta na gyara gida, wanzar da hadin kai da kawar da sabani a ciki, domin kara karfin jam’iyya kafin babban zaben 2027.


Follow Us