Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 9 Satumba, 2025
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Radda (PhD), ya jaddada kudirin gwamnatinsa na ƙarfafa zaman lafiya da ci gaba mai ɗorewa, yayin da ya kaddamar da shirin Conflict Prevention, Crisis Response and Resilience (CPCRR), wani shiri da Tarayyar Turai (EU) ke tallafawa da kuɗin da ya kai Euro miliyan biyar, a Katsina ranar Litinin, 9 ga Satumba, 2025.
Da yake jawabi a dakin taro na Hillside Hotel da ke Katsina, Gwamna Radda ya bayyana yadda haɗuwar hare-haren ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, rikice-rikicen ƙabilanci, sauyin yanayi, raguwar tattalin arziƙi, da rashin aikin yi suka durƙusar da al’ummomi a faɗin jihar.
“A Jibia da sauran wuraren da abin ya shafa, an rufe makarantu, an daina noma, kasuwanni sun tsaya, yara sun rasa ilimi, iyaye suna binne ‘ya’yansu, dattijai sun rasa gidajen kakanninsu. Waɗannan ba matsaloli ne daidaiku ba, matsaloli ne da suka haɗe wuri guda waɗanda ke buƙatar haɗin gwiwa wajen magance su,” in ji gwamnan.
Shirin CPCRR na tsawon watanni 18, zai gudana a kananan hukumomi guda takwas da ke cikin haɗari a Katsina da akalla biyu a Zamfara, wanda aka gina shi a kan ginshiƙai uku, da suka haɗa da, Ƙarfafa zaman lafiya da rage rikici, Ƙarfafa tattalin arziƙi da samar da ayyukan yi da kuma Ƙarfafa shugabanci da hukumomi
Gwamna Radda ya jaddada cewa wannan shiri ba zai kasance “shiri daga sama zuwa ƙasa” ba, sai dai shiri na al’umma wanda za su jagoranta da kansu, tare da shigar da mata, matasa da kuma masu nakasa cikin tsari da aiwatarwa. Ya bayyana cewa Katsina ta samu nasara wajen warware rikice-rikice a kananan hukumomi hudu, kuma tattaunawa na ci gaba a wasu biyu, tare da ƙara tabbatar da cewa CPCRR ya ginu ne a kan shirin warware rikici da sasancin al’umma wanda EU ta tallafa a baya.
Don tabbatar da ingantacciyar gudanarwa, gwamnan ya sanar da kafa Kwamitin Jagoranci na CPCRR, wanda shi kansa zai jagoranta, tare da haɗa kwamishinonin muhimman ma’aikatu irin su tsaro, noma, muhalli, ilimi, shari’a, harkokin mata da kananan hukumomi.
“Wannan ba kwamitin shan shayi ba ne,” in ji shi. “Kwamitin aiki ne mai cikakken iko da alhakin tabbatar da gaskiya, amana da shugabancin al’umma.”
Ya roƙi shugabannin gargajiya da na addini da su ci gaba da amfani da tasirinsu wajen wanzar da zaman lafiya da haɗin kai, tare da kira ga matasa da mata da su fita daga kasancewa waɗanda rikici ke cutarwa kawai, su koma masu kawo sauyi. Ya yaba wa jami’an tsaro bisa sadaukarwarsu, sai dai ya yi gargaɗi cewa ba za a samu ɗorewar zaman lafiya ta hanyar yaƙi kaɗai ba tare da tattaunawa, ci gaba, da gina amana ba.
“Manufarmu ita ce mu gina Katsina wadda zaman lafiya ba kawai rashin tashin hankali ba ne, ya kasance adalci, dama, da haɗin kai. Wannan shiri ba sihiri ba ne, kawai mataki ne mai muhimmanci zuwa wannan makomar,” in ji Radda, inda ya yi alkawarin haɗa kuɗaɗen gwamnati da tallafin ƙasa da ƙasa.
Gwamnan ya gode wa Ƙungiyar Tarayyar Turai, Hukumomin Duniya irin su (IOM), Mercy Corps, CDD da sauran abokan hulɗa bisa goyon bayansu.
A jawabinsa Jakadan Tarayyar Turai a Najeriya, Gautier Mignot, ya jaddada kudirin ƙungiyar wajen tallafawa zaman lafiya, tsaro, da ci gaba mai ɗorewa a Katsina da Arewa maso Yamma baki ɗaya.
Ya tuna cewa haɗin gwiwar EU da Katsina tun daga shekarun 1990s ya taɓa shafar yaki da talauci, kare muhalli, makamashi mai sabuntawa da ilimi, inda ya kawo misali da Shirin Gandun Daji na Katsina da kuma Shirin Inganta Ban-Ruwa na Katsina.
“Yau mun dawo tare da abokan hulɗarmu don tabbatar da cewa EU na da cikakken goyon baya ga ci gaban Najeriya mai ɗorewa, tsaro da walwala. Zaman lafiya da tsaro ginshiƙai ne na ƙimar Turai, kuma dole mu ƙarfafa juriyar al’umma,” in ji Mignot.
Ya bayyana cewa CPCRR ya ginu a kan nasarorin shirin EU na baya, ciki har da STEM-CNCR da aka kammala kwanan nan, wanda za a aiwatar a Katsina da Zamfara tare da haɗin gwiwar IOM, Mercy Corps, da CDD.
Mignot ya jaddada muhimmancin sanya mata, matasa, yara da masu nakasa a tsakiyar dukkan ayyukan zaman lafiya.
“A mafi yawan lokuta, maza ne ke haddasa rikici. Amma babu zaman lafiya ba tare da mata ba. Waɗannan rukuni ne da rikici ke fi cutarwa, amma su ne ginshiƙan canji da cigaba,” in ji shi.
Jakadan ya nuna damuwa kan tabarbarewar rashin abinci mai gina jiki a Arewa maso Yamma da Arewa maso Gabas, wanda ke barazana ga rayukan dubban yara. Ya tuna da ziyarar da ya kai cibiyoyin kula da yara masu fama da rashin abinci a Sokoto a watan Yuli tare da Ministan Harkokin Jinƙai na Tarayya, inda ya bayyana halin da ake ciki a matsayin “abin takaici.”
“A Katsina, EU na ba da tallafin Euro miliyan takwas ta hannun abokan hulɗa kamar Médecins Sans Frontières (MSF) domin kula da yara masu fama da rashin abinci a cibiyoyi ciki har da Asibitin Turai Yar’adua. Amma ana buƙatar mataki cikin gaggawa, ba wai kawai don ciyar da yara yau ba, har ma don hana sake faruwar matsalar a badi,” in ji Mignot.
Ya tabbatar da cewa EU za ta ci gaba da aiki tare da Gwamnatin Jihar Katsina da abokan hulɗa wajen samar da mafita na dogon lokaci a fannin zaman lafiya, tsaro da wadata.
Sauran masu jawabi a wajen kaddamarwar sun haɗa da Kwamishinan Tsaron Cikin Gida na Katsina, Dr. Nasir Mu’azu Danmusa, wanda ya danganta yawan rikice-rikice da kwadayi, hassada, rikice-rikicen amfani da albarkatu da sauyin yanayi da rashin adalci. Ya ce gwamnati a ƙarƙashin jagorancin Radda ta ‘yantar da kananan hukumomi hudu daga hannun ‘yan bindiga cikin watanni takwas, tare da fatan shirin CPCRR zai shimfiɗa zaman lafiya a sauran wurare.
Kwamishinar Harkokin Mata, Hajiya Hadiza Yar’adua, da Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin masarautu, Alhaji Bishir Tanimu Gambo, Kwamishinan raya karkara da ci-gaba Farfesa Abdulhamid Ahamd, suma sun yi tsokaci kan muhimmancin haɗa mata da al’ummomin karkara cikin shirin.
Taron ya samu halartar jakadun ƙasashen waje, kungiyoyin ƙasa da ƙasa, shugabannin gargajiya, wakilan al’umma da manyan jami’an gwamnati, dukansu na mai da martani da goyon baya ga nasarar shirin.