Hamshakin dan kasuwa, manomi kuma jigon ɗan siyasa a jihar Katsina, Hon. Hamza Sule Faskari, ya raba tallafin azumin Ramadan ga ƙungiyoyi daban-daban waɗanda suka haɗa da marayu da zaurawa da 'yan gudun hijira da marasa galihu, game da 'yan siyasa da ƙungiyoyin matasa da ƙungiyoyin cigaban al'umma daga ƙananan hukumomi 11 na yankin Funtua.
Kayayyakin da darajarsu ta kai Naira miloyin 60, sun haɗa da buhunan shinkafa 400, da buhunan gero 500, da buhunan masara 300, da kuma tallafin kuɗi na Naira miloyin 62 da aka raba ma al'umma domin su samu sauki a wannan watan na Ramadan.
Hamza Sule wanda shine Wamban Faskari kuma Sadaukin Kasar Hausa, shi ne kuma Kwamishinan Muhalli na Jihar Katsina, inda ake yaba masa kan ƙoƙarinsa na aiwatar da tsare-tsaren gwamnatin Malam Dikko Radda a wannan mihimmin bangaren.
A taron wanda ya gudana a garin Faskari, wanda dubun dubatar masu cin gajiyar tallafin suka halarta, Hon. Hamza Sule ya ce ya raba tallafin ne domin taimakawa al'umma da kayan masarufi da kudi domin su samu saukin yin ibada a wannan watan mai alfarma.
Ya yi amfani da wannan damar wajen yin kira ga jama'a da su kara himma wajen gabatar da aiyukan ibada da addu'o'i don samun zaman lafiya da walwala a jihar Katsina, kana ya bukace su su yi wa shugabanni a dukkan matakai addu'a domin samun nasarar kawo cigaba mai dorewa a jihar.
Shi ma Mataimakin Shugaban jam'iyyar APC a Jihar Katsina, Hon. Bala Abu Musawa, ya ce Hamza Sule na cikin jiga-jigan jam'iyya da ke sahun gaba wajen tallafa ma 'ya'yan jam'iyya akai-akai, wanda ke kara ma jam'iyyar farin jini a jihar.
Ya ce duk Ramadan da kuma a mihimman lokuta sai Hon. Hamza Sule ya taimaka ma 'ya'yan jam'iyya da marasa galihu, yace hakan na kara musu biyayya ga jam'iyya da kuma taimakawa ga cin nasararta a yayin zabuka.
Shugabannin gargajiya, da malamai da limamai, da abokan arziki da suka yi jawabi a wurin taron sun yaba wa Hon. Hamza Sule kan wannan tallafin yayin da suka bukaci sauran 'yan siyasa da 'yan kasuwa da su yi koyi da wannan farin halin.
Shugaban Karamar Hukumar Faskari, Alh. Surajo Aliyu Daudawa a nasa jawabin, yace karamar hukumar zata cigaba da biyawa al'ummar karamar hukumar kudin wuta tsawon shekara guda don su samu sauki.
//////