ANYI KIRA GA MABIYA AHLUL BAITI DA SU FITO SU YANKI KATIN RIJISTAR ZABE

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes07092025_115732_Screenshot_20250907-125624.jpg

 
Daga Muhammad Sakafa, Kano 
     
Wannan kiran ya fito ne daga bakin Shugaban Gamayyar kungiyar mabiya da masoyan Ahlul Baiti (AS) ta kasa reshen jihar Kano, wadda aka fi sani da AHLUL BAITI NAJERIYA, Hon. Adamu kabiru (Auduwa) a wata zantawa da yayi da manema labarai a Kano.  

Honourable Adamu Kabiru, ya Kara da cewa " muna Kira da dukkan mabiya da masoyan Ahlul Bait na kasar nan da su dukufa wajen zuwa yankar Katin rijistar zabe don samun damar Kada kuri'a a dukkan matakai na zabuka masu zuwa.
     
Shugaban na gamayyar ya Kara da cewa "wannan wata dama ce a yanzu na fitowar dukkan mabiya Ahlul baiti don yankar Katin zaben duba da irin yawan adadin da muke da su na mabiya na Ahlul bait (as) a Fadin kasar nan, ganin yanzu aikin yana Kan gudana a dukkan ofisishin zabe na dukkan kananan hukumomin 774 na Fadin kasar nan. 

Don haka dukkan Wanda ya San bashi da Katin zaben a baya ko kuma Wanda nashi karin ya bace ko matasan da a shekarun da aka yi aikin Katin zaben shekarunsu Basu Kai ba, Amma yanzu shekarunsu sun Kai mazansu da mata da su gaggauta yankar Katin zaben su Adana Shi zuwa lokacin zabuka masu zuwa. 

Daga karshe idan  lokacin zabe ya zo ne za a ji matsayarmu ta Wanda zamu kadawa kuri'unmu ga  Wanda Zai Kare mana mutumcinmu da fahimtarmu ta addini da kuma wasu hakkokinmu da kowanne dan kasa ke  da Shi, Wanda kundin tsarin Mulkin kasar nan ya bamu". Inji Shi.

Follow Us