Babban Kwamandan Sojojin Ƙasa Ya Kai Ziyara Katsina, Ya Nemi Ƙarin Haɗin Kai Domin Yaƙi da ’Yan Bindiga

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes25082025_202912_FB_IMG_1756153691997.jpg

Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times | 25 ga Agusta 2025

Babban Hafsan Sojojin Ƙasa na Najeriya (COAS), Laftanar Janar Olufemi Oluyede, a ranar Litinin ya kai ziyarar ban girma fadar Gwamnatin Jihar Katsina, inda ya yi kira da a ƙarfafa haɗin kai tsakanin jami’an tsaro, gwamnati da al’umma wajen yaƙi da ta’addanci da ’yan bindiga a fadin jihar da kasa baki ɗaya.

An tarbe shi a madadin Gwamna Dikko Umaru Radda daga mataimakin gwamna, Malam Faruq Lawal Jobe. Janar Oluyede ya ce, wannan ziyara tana cikin al’adar soja ta nuna ban girma ga shugabannin al’umma tare da ƙarfafa dangantaka domin cimma zaman lafiya.

A jawabinsa, Janar Oluyede ya yaba wa mutanen Katsina bisa “goyon baya na musamman” da suke bai wa dakarun da ke aiki a sassan jihar.

“An san Katsina da karamci da goyon baya ga sojoji. Amma ina ganin wajibi in mika ta’aziyyarmu bisa asarar rayuka a hare-haren baya-bayan nan. Wannan abu ne mai matuƙar takaici da baƙin ciki, amma ya ƙara mana ƙwazo wajen tabbatar da tsaron jihar,” in ji shi.

Ya jaddada cewa tsaro aikin kowa ne, inda ya bayyana cewa ko da yake dakarun soji suna ƙoƙarin kare rayuka, babu makawa sai da gudummawar al’umma musamman ta fannin bayanan sirri.

“Gaskiyar magana, muna yaƙi da ’yan Najeriya ’yan’uwarmu ne. Makiyan suna cikinmu. Ya zama wajibi mu gano waɗannan makiyan jiharmu mu hukunta su yadda ya kamata. Tsaro aikin kowa ne, kuma ba tare da haɗin kai ba za mu iya samun zaman lafiya ba,” in ji shi.

Janar Oluyede ya ce ya riga ya yi tattaunawa ta musamman da shugabannin jihar kan batun tsaro, tare da tabbatar da cewa rundunar sojojin ƙasa za ta ƙara ƙaimi a ayyukanta domin tabbatar da tsaro a Katsina da sauran jihohin ƙasar.

“Na tabbata shugaban ƙasa ya kuduri aniyar ganin Najeriya ta zama mai tsaro. Amma dole ne mu yi aiki tare da jama’a. Rundunar sojoji rundunar al’umma ce, kuma idan aka ba mu goyon baya, za mu iya tabbatar da tsaro a Najeriya cikin nasara,” ya ƙara da cewa.

A nasa jawabin, Mataimakin Gwamna, Malam Faruq Lawal Jobe, ya gode wa babban hafsan sojojin ƙasa bisa ziyarar ban girman, tare da tabbatar masa da cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da ba da haɗin kai ga jami’an tsaro.

“Gwamnati da al’ummar Katsina suna godiya bisa sadaukarwar rundunar soji da sauran jami’an tsaro. Muna tabbatar muku da goyon bayanmu domin tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyin jama’a a jihar,” in ji shi.

Da yake jawabi ga manema labarai a fadar gwamnatin jihar bayan ganawar da gwamnatin jihar, babban hafsan sojoji ya jaddada cewa manufar ziyarar tasa ita ce mika ta’aziyya bisa hare-haren da suka yi sanadiyyar rasa rayuka, gode wa al’umma bisa goyon bayan da suke bai wa sojoji, tare da yi musu alkawarin ƙarin zage Dantse a gaba.

“Wannan babban rashi ne ga kowa, abin bakin ciki ne. Amma ina tabbatar muku cewa rundunar sojoji za ta ƙara jajircewa wajen kare Katsina da sauran jihohin ƙasar,” in ji shi.

Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da jihar Katsina ke ci gaba da fuskantar matsalar tsaro musamman a karkara. A satin da ya gabata, al’ummar Mantau dake gundumar Ƙarfi, ƙaramar hukumar Malumfashi, sun shiga cikin jimami bayan ’yan bindiga suka kai mummunan hari ga masallata da asubahi inda, suka kashe mutane da dama a abin da ya jefa jihar cikin damuwa da jimami. 

Wannan mummunan hari da ya girgiza jihar ya haifar da ƙorafi daga jama’a da kira ga hukumomin tsaro da su ƙara ɗaukar matakai masu tsauri domin kawo ƙarshen kashe-kashe, garkuwa da mutane da lalata rayuwar al’umma a Katsina da sassan arewacin Najeriya.

Follow Us