Daga wakilanmu
Habib kamar yadda sunansa na yanka, yake amma kamar yadda dabi un 'yan kungiyar boko haram take suna da wani lakabi da suke baiwa junansu.
Habib yana daga cikin kananan 'ya'ya da Muhammad Yusuf ya mutu ya bari. Sunan uwarsa Hafsat amma ana kiranta da Ummi.
Bayan kashe Muhammad Yusufu tayi gudun hijira da danta yana karami Habib zuwa kasar chadi. Daga baya Shekau ya maido cikin dajin sambisa yayi niyyar aurenta, amma taki yarda.
Ummi ta auri daya daga cikin kwamandojin shekau kuma almajirin Muhammad yusufu wanda ake kira Mamman Nur.
Habib ya tashi a cikin dajin sambisa tsakanin mayakan boko haram yayi karatu a gaban almajiran mahaifinshi inda ya hardace alkur ani, ya iya harsunan larabci, faransanci, Hausa, da kuma Barbarci yaren uwayenshi.
Wata ruwayar tace yayi tafiya zuwa kasashen waje daga dajin sambisa inda ya koyo harkar daukar makami da sarrafa jirgi maras matuki da kuma inji mai kwalwa.
Bayan kashe Mamman Nur a fadan cikin gida, Habib ya dawo sambisa wajen wanda Albarnawi wanda yake rike da wani sashe na boko haram.
Boķo haram bangaren albarnawi wanda yake yana cikin 'ya'yan Muhammad yusuf suna ta karfafa ikon su a yankin sambisa da kuma gefe da tekun chadi.
Rahotanni sunce an tura Habib ne can domin ya jagoranci wani sabon reshe na boko haram da aka kafa.
An kama "yan boko haram din da farko a matsayin wasu 'yan fashi da makami a watanni baya, har jaridun kasar suka sanya hotunansu.
Wani dan jarida daga Najeriya shine wanda yayi binciken kwakwaf din da ya bayyana cewa wadanda aka kama 'yan boko haram ne kuma daya daga cikin su dane ga Muhammad yusuf wanda ya kafa kungiyar boko haram.
Kama Habib ya girgiza duniyar masu ikirarin jihadi irin na boko haram, domin rahotanni sunce yaro ne mai hazaka da kuma gaskiya da ibada suna da guri akan shi.
Katsina times
@ www.katsinatimes.com
Facebook page : katsina city news
Jaridar Taskar labarai labarai
Facebook page: Jaridar Taskar labarai
07043777779.