Gidauniyar Lado Na Shirin Tallafa Wa Dalibai 2,000 a Jami’ar UMYU, Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes20082025_120951_FB_IMG_1755691740509.jpg



Daga wakilinmu | Katsina Times 

Gidauniyar Cigaba ta Lado (Lado Development Foundation) ta sake tabbatar da jajircewarta wajen tallafawa fannin ilimi, inda ta bayar da dubban tallafin karatu ga ɗaliban Jami’ar Umaru Musa Yar’adua (UMYU), Katsina.

An gudanar da tantancewar a ranar Talata, 19 ga Agusta, 2025, inda ɗalibai da dama suka halarta domin neman cancanta. Sunayen waɗanda suka samu nasara za a fitar da su a ranar Laraba, 20 ga watan Agusta, tare da biyan kuɗin makaranta ga waɗanda aka zaɓa.

Mai shirya ayyukan Gidauniyar, Kwamared Gali Salisu Bakori, ya bayyana cewa an ƙirƙiri shirin ne domin tallafawa ɗalibai marasa galihu da masu buƙata ta musamman a faɗin ƙasar.

“Mun riga mun kai irin wannan tallafi zuwa makarantu daban-daban a ƙasar nan. A nan Jami’ar Umaru Musa Yar’adua kaɗai, ɗalibai 372 sun amfana a 2023, 813 a 2024, sannan 1,113 a zangon farko na 2025. A bana kuma burinmu shi ne sama da ɗalibai 2,000 su amfana,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, wasu jami’o’i irin su Bayero University Kano (BUK) suma suna daga cikin waɗanda suka ci gajiyar shirin.

Registrar na Jami’ar Umaru Musa Yar’adua, Malam Muhammad Yusuf, wanda ya wakilci Shugaban Jami’ar, Farfesa Shehu Salihu Muhammad, ya jinjinawa Gidauniyar bisa wannan ƙoƙari mai amfani.

Ya ce: “Wannan shiri ba wai ga jami’a kaɗai yake amfani ba, har ma ga al’umma baki ɗaya. Duk wanda Allah Ya hore masa baiwa wajibi ne ya taimaka wa wasu. A matsayimmu na Musulmi kuma Hausawa, mun yi imani da taimakon juna da ɗaukar nauyin al’umma.”

Registrar ɗin ya bayyana cewa shirin ya yi daidai da manufar gwamnatin Jihar Katsina, kasancewar jami’ar ta karkashin ikon gwamnatin jihar, kuma hakan zai rage nauyin kuɗin makaranta daga iyaye.

Ya kuma tabbatar da cewa jami’ar, ta hanyar Ofishin Dean na Harkokin Dalibai, za ta yi aiki tare da Gidauniyar domin tabbatar da sahihancin sunayen waɗanda suka cancanta.

Gidauniyar Lado, wacce Alhaji Yakubu Lado Danmarke ya kafa, ta zama ginshiƙin bege ga ɗalibai marasa galihu a faɗin Najeriya.

Ta hanyar tallafin karatu da shirye-shiryen ilimi daban-daban, Gidauniyar na ci gaba da rufe gibin kuɗi da samar da daidaitatton damar ilimi ga kowa, lamarin da ke kafa sabon tarihi a fagen tallafawa ɗalibai a Jihar Katsina da ma ƙasar baki ɗaya.

Follow Us