KATSINA TIMES.
A cikin wata hira da ya yi da manena labarai, a ranar Juma'a 15 ga watan Augusta 2025, Alhaji Sanusi Kabir Usman, wanda shi ne shugaban kungiyar ta kwallon kafa ta Folo a jihar Katsina, ya bayyana irin rawar da jihar Katsina ta taka wajen kafa tarihin fara zama jaha ta farko da ta fara buga wasan.
"Wannan wasa na wannan shekarar abinda ya sanya muka sanya mashi wannan suna shine domin tunawa kakanmu, Sir. Usman Nagogo, saboda shi ne na farkon wanda ya fara kirkiran Nigerian Polo Association, idan ka duba daga sadda ya kirkiro shi zuwa yanzu shekara dari kenan"
Ya kara da cewa "cikin cigaban da aka samu game da wasan folo a jihar katsina zaka ga shekara 20 baya ba haka yake ba, idan ka duba irin gine ginen da muka yi, da yan wasan da muke da su, zaka ga yasha banban da na da, saboda haka an samu cigaba sosai a wasan folo a Katsina." inji shi.
Haka zalika ya cigaba da cewa "Daga gobe Asabar har tsawon sati guda za'a cigaba da ganin manyan baki na ta shigowa jihar Katsina, domin halartar wasan, ya kara da cewa akalla abokan takara ashirin da shidda ne zasu kara da junan su a yayin wasan.
Daga karshe ya shawarci masu zuwa kallon wasan da su bi a hankali wajen kokarin shiga wajen kallon wasan, duk da cewa a bana an samar da tsari sosai wanda zai taimaka ma masu zuwa kallon.