Kungiyar "Good Governance Club" Ta Ziyarci Hukumar KASSROMA, Ta Kuma Jaddada Ƙudurinta Na Saya Wa Gwamna Radda Tikitin Tsayawa Takara a Zaben 2027.

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes31072025_213551_FB_IMG_1753997684007.jpg


‎Daga Muhammad Ali Hafizy, Katsina Times.
‎Kungiyar Good Governance Club wadda take rajin tabbatar da shugabanci na gaskiya, a karkashin jagorancin shugaban kungiyar, Comrd Shehu Usman Yusuf Kofar Soro, ta ziyarci shugaban hukumar kula da kuma gyara hanyoyi ta jihar Katsina. Engr. Surajo Yazid Abukur, tare da karrama shi da lambar yabo a matsayin wanda ya samar da cigaba a cikin al'umma.
‎Ziyarar wadda ta gudana a ranar Alhamis 31 ga watan Yuli na shekarar 2025, a shelkwatar hukumar dake Katsina, ta samu jagorancin kungiyar Good Governance Club, tare da rakiyar wasu wakilai daga cikin kungiyoyin al'umma.
‎Comrd Shehu Kofar Soro a jawabin da ya gabatar yayin ziyarar, ya jaddada kudurin kungiyar da yake jagoranta na zama ƙungiya ta farko da tayi yunkuri tare da shelanta cewa zata saya ma gwamna Radda tikitin tsayawa takarar gwamnan jihar Katsina a zabe mai zuwa na 2027.
‎"Gwamna Radda, gwamna ne na al'umma, kuma cigaban da ya kawo wa jihar Katsina ba karami bane, shiyasa wannan kungiyar ta Good Governance Club taga dacewa ta saya mashi tikitin tsayawa takara a zabe mai zuwa na 2027, domin ya ci gaba da ayyukan alkairin da yake yi wajen samar wa jihar Katsina ci-gaba mai ɗorewa" inji shi.
‎Ya kara da cewa "Hukumar KASROMA a jihar Katsina, ta samu kyakkyawan sauyi ta dalilin samun jagoranci na gari a karkashin shugaban hukumar Engr Surajo Yazid Abukur" ya ce, Hukumar ta samar wa al'ummar jihar Katsina hanyoyi masu kyau tare da tabbatar da kiyaye abubuwan da suke sanya aukuwar hadari a kan tituna. Inji shi.
‎Shugaban hukumar KASSROMA ta jihar Katsina, Engr Surajo Yazid Abukur. Ya yi jinjina ta musamman ga kungiyar, tare da tabbatar masu da cewa zai kasance a tare da su, da kuma tabbatar da cigaba jihar Katsina a karkashin jagorancin gwamna Malam Dikko Umar Radda.
‎Ya kara da cewa, Shugabancin Malam Dikko Umar Radda shugabanci ne na gari, kuma shugabanci ne wanda za'a yi fatan dorewar shi, ya yi godiya ga kungiyar akan yunkurin da suka yi na saya wa gwamna tikitin tsayawa takara a 2027.
‎"Ayyukan da hukumar KASSROMA ke gabatarwa, ayyuka ne wanda gwamna Radda ya bada umarnin aiwatar dasu, kuma gwamna ya hore mu da mu cigaba da sauran koken al'umma da kuma tabbatar da cewa munyi masu abinda ya dace" inji shi.

Follow Us