Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya bayyana alhinin sa kan rasuwar fitaccen ɗan jaridar nan, Dakta Leon Habby Usigbe, wanda ya kasance shugaban jaridar Nigerian Tribune a Abuja.
A cikin wata sanarwa ta ta'aziyya da ya fitar a ranar Asabar, 26 ga Yuli, 2025, Ministan ya bayyana marigayin a matsayin “ɗan jarida na ƙwarai, ƙwararre mai kaifin basira, kuma haske a fagen aikin jarida a Nijeriya.”
Ya ce ayyukan Usigbe sun bayyana gaskiyar sa, zurfin sa a tunani, da jajircewar sa wajen kare muradun jama’a.
Ya ce: “A matsayin sa na ɗan jarida mai amfani da alƙalamin sa wajen kare dimokiraɗiyya da cigaban ƙasa, ya riƙa kawo bayanai masu zurfi, ilimi, da daidaito a cikin rahotannin sa. A cikin sa, 'yan jarida sun samu ɗan ƙasa nagari wanda ya yi amfani da sana’ar sa wajen bunƙasa gaskiya da cigaban ƙasa."
Idris ya kuma tuna yadda Usigbe ya riƙa bayar da gagarumar gudunmawa a tarukan manema labarai da ma a Fadar Shugaban Ƙasa, yana cewa, “Shiga tsakani da ya riƙa yi a irin waɗannan taruka na manema labarai na haɓaka ingancin muhawara, ya kuma taimaka wajen ƙarfafa alaƙa tsakanin gwamnati da 'yan jarida — duk da nufin samar da al'umma mai wayewa tare da fahimtar juna.”
Ya ce rasuwar Dakta Usigbe babban rashi ne ba kawai ga kamfanin jaridar Tribune da fagen aikin jarida ba, har ma da ƙasar nan baki ɗaya.
“Nijeriya ta yi rashi matuƙa — mun rasa ɗaya daga cikin fitattun 'yan jarida, wanda ilimin sa, jarumtar sa, da himmar sa ta sa kowa yana girmama shi.”
A madadin Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Idris ya miƙa ta’aziyyar sa ga shugabanni da ma’aikatan Tribune, da gwamnati da al’ummar Jihar Edo inda marigayin ya fito, da kuma iyalan sa, da abokan sa, da ma dukkan masu mu’amala da shi.
“Allah ya jiƙan sa, ya ba duka waɗanda ya bari haƙurin jure wannan babban rashi,” inji Ministan.