Daga wakilinmu @ Katsina times
Kansila mai wakiltar unguwar Musawa a karamar hukumar musawa, Umar sa'adu, ya rubuta wata takardar korafi akan rabon takin karamar hukumar Musawa.
Takardar wadda ya rubuta korafin, akan Babban jami in rabon takin na karamar hukumar Musawa mai suna Sani Yahaya.
Takardar kamar yadda wakilan Katsina Times suka gani an yi kwafin ta ga jami ai da ofisoshi daban daban,ciki har da kwamishinan gona na jahar Katsina da kwamishinan yan sanda da jami an DSS.
Korafin dake a cikin takardar kamar yadda katsina time suka gani.tayi zargin
Shugaban rabon yakin Sani Yahaya, baya tuntubar kowa a wajen aikin rabon takin, yana gaban kansa ne, shi daya.yana abin da yaso ne, ba tare da shawartar sauran yan kwamitin ba.
Kansilan,yayi zargin cewa,an ,kayyade kowace rumfar zabe a karamar hukumar musawa, za a bada taki buhu sittin,(60)amma shi,buhu ar ba in,(40) ya bayar ..ba a san inda ya kai buhu 540 da sukayi rara ba.
Kansilan yayi zargin cewa,kwamitin rabon takin ya amince a karbi dari biyar akan kowane buhu a matsayin kudin hidima,amma ya rika karbar Naira dubu daya da dari biyar.babu wanda yasan ya yayi da Naira dubu daya da ya dora ba, wanda kudin sun kai Naira milyan daya da dubu dari shidda.
Kansilan yayi zargin cewa akwai wasu awaki da akace za a raba .amma har yanzu shiru kakeji akan maganar su.
Kansilan yayi zargin cewa akwai takin da Mai girma gwamna yace za a raba ma, manyan manoma shima har yanzu, jami in rabon takin na Musawa baiyi maganar su ba.
Kansilan ya roki mai girma gwamnan ya sa ayi bincike mai zaman kanshi akan wadannan zarge zarge.
Jaridun Katsina times sun tuntubi jami in rabon takin,sani Yahaya da ake zargi.sani Yahaya ya karyata duk zarge zargen ya kuma ce yana da maraba da duk wani bincike mai zaman kanshi da za a yi, yace a shirye yake ya bada hadin kai.
Yace tabbas an rage taki, amma su "yan kwamitin sune suka yarda a rage takin kuma suka ce a maido yadda yake kuma aka maido.
Yace akan kudi 1500 da akace an sanya, wannan ba gaskiya bane, dari biyar 500 aka sanya kuma har yanzu kudin na hannun shi kansilan da yayi korafin.Ban amshe su ba.ya kuma karyata ya amshi dubu daya a hannun kowa.
Jami'in yace duk abin da zaiyi yana tafiya kafada da kafada da sauran membobin kwamitin shi.yace kuma yayi imanin zasu tabbatar da maganar shi.
@Katsina times
Www.katsinatimes.com