Matashi Ya Kashe Maƙwabcinsa Saboda Rigimar Igiyar Shanya a Katsina

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes04072025_161208_FB_IMG_1751645477703.jpg


Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times

Wani matashi mai shekaru 35 da haihuwa, mai suna Aminu, ya daba wa maƙwabcinsa Malam Masa’udu, mai shekaru 45, wuƙa har lahira sakamakon wata rigima da ta samo asali daga amfani da igiyar shanya kaya a birnin Katsina.

Lamarin mai tayar da hankali ya faru da yammacin Alhamis, 3 ga Yuni, 2025, a unguwar Ministerial Quarters da ke kusa da Fatima Shema Estate, inda duka biyun ke gudanar da sana’ar wanki da guga.

Ganau sun shaida wa Katsina Times cewa rikicin ya samo asali ne daga igiyar da Malam Hassan ya daura domin amfanin jama'a. Marigayi Masa’udu ya nemi amfani da igiyar amma Aminu ya hana shi, yana ikirarin cewa ba shi da ikon shanya kaya a wurin.

“Ya roƙi a bar shi ya shanya kayan na ɗan lokaci, amma Aminu ya ƙi, ya jefar da kayan ƙasa sannan ya tattaka su,” in ji Malam Hassan, wanda ya mallaki igiyar.

Bayan haka, Malam Masa’udu ya shiga wani shago yana bayyana abin da ya faru, amma Aminu ya biyo shi da wuƙa cikin fushi. Duk da cewa Masa’udu ya yi ƙoƙarin tserewa, Aminu ya bi shi har ya cimma shi, inda ya daba masa wuƙa, wasu ganau sun ce har sau bakwai.

An garzaya da shi zuwa Asibitin K-Dara da taimakon jami’an NSCDC, amma ya rasu kafin a kai shi asibiti. Daga bisani aka mayar da gawarsa zuwa babban Asibitin Katsina, inda DPO na ‘yan sanda na Charanchi tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na Batagarawa suka cafke wanda ake zargi.

A ranar Juma’a, 4 ga Yuni, aka yi jana’izarsa a gidansa bisa ga tsarin addinin Musulunci.

Binciken Katsina Times ya gano cewa ba wannan ne karo na farko da ake samun rashin jituwa tsakanin Aminu da marigayin ba. A bara kafin watan azumin Ramadan, Aminu ya kai Malam Masa’udu kotu bisa zargin ya yi masa sharri da zargin Luwadi, amma kotu ta yi watsi da karar saboda rashin hujja.

Marigayin, wanda asalin dan karamar hukumar Kaita ne, ya shafe shekaru da dama a unguwar Ministerial Quarters kuma ya kasance mutum mai gaskiya da amana. Shi ne ke kula da shagunan haya, lissafin kudin wuta da sauran muhimman al’amura a wajen. Haka kuma, shi ne ya bai wa Aminu shagon da yake haya kafin afkuwar kisan.

Malam Masa’udu mai ruwa ya bar mata ɗaya da rababben Goro, da ‘ya’ya shida, yayin da Aminu, wanda ba shi da aure, ke tsare a hannun rundunar ‘yan sanda ta jihar Katsina yayin da ake ci gaba da bincike.

Follow Us