Daga Wakilin Mu
Ƙungiyar Citizens Participation Against Corruption Initiative (CPACI) ta bayyana gamsuwa da irin ci gaban da Gwamnatin Jihar Katsina ta samu a cikin shekaru biyu na mulkin Gwamna Dikko Umar Radda.
Ƙungiyar ta bayyana hakan ne a taron tattaunawa da masu ruwa da tsaki da aka gudanar a ranar Alhamis, 29 ga Mayu, 2025, a dakin taro na cibiyar 'yan jarida ta ƙasa (NUJ) da ke cikin birnin Katsina.
A jawabinsa na buɗe taro, Shugaban CPACI, Kwamared Bishir Dauda Sabuwar Unguwa, ya marabci mahalarta, tare da gabatar da cikakken jawabi kan ci gaban dimokuraɗiyya da ayyukan raya ƙasa da aka samu tun daga lokacin da Gwamna Radda ya hau mulki.
Kwamared Bishir ya yabawa Gwamnan bisa yadda ya mayar da hankali wajen aiwatar da muhimman ayyuka da sauye-sauye a fannoni da dama kamar tsaro, ilimi, noma da kiwon lafiya. Ya bayyana mulkin shekaru biyu na Gwamna Radda a matsayin wanda ya cancanci yabo bisa tsare-tsaren da suka mayar da hankali kan bukatun al'umma da ci gaban ababen more rayuwa.
Taron ya samu halartar wasu manyan jami'an gwamnati da suka haɗa da Darakta Janar na Hukumar Tara Haraji ta Jihar Katsina, Dr. Kabir Abdullahi Yantumaki, da kuma Sakataren Hukumar Yaƙi da Cin Hanci ta Jihar Katsina, Dr. Jamilu Muhammad Charanchi, waɗanda suka yi tsokaci kan nasarorin da aka samu a hukumominsu da kuma tasirin shugabancin Gwamna Radda a fadin jihar.
A jawabansu, jami’an sun bayyana Gwamna Radda a matsayin ɗaya daga cikin shugabannin da suka fi kowa tasiri a tarihin jihar, suna mai jaddada yadda yake jagorantar jihar bisa gaskiya da tsare-tsaren ci gaba masu ɗorewa. Sun kuma yi fatan Allah ya kara masa nasara da zaman lafiya a cikin mulkinsa.
Taron ya ƙare da zama na tattaunawa tsakanin jami’an gwamnati da jama’ar da suka halarta, inda aka bai wa mahalarta damar tambaya kai tsaye, kuma an samu amsoshi masu gamsarwa da ƙarfafa gwiwa ga al’umma.
Mahalarta taron sun fito ne daga sassa daban-daban na jihar, ciki har da kungiyoyin matasa, ƙungiyoyin mata da wakilan ƙungiyoyin farar hula, wadanda suka hallara domin tantance nasarorin da gwamnati mai ci ta samu cikin shekaru biyu da suka wuce.