Auwal Isah Musa | Katsina TIMES
Shugaban kungiyar Dikko Project Movement, Dr Musa Yusuf Gafai, ya jagoranci rangadin duba aikin da aka kammala na titin Eastern Bypass da ke Katsina, a wani bangare na kokarin bayyana wa jama'a irin ci gaban da gwamnatin Malam Dikko Umaru Radda ke samu a fannin ayyukan raya kasa. Rangadin ya gudana ne da yammacin ranar Juma’a, tare da hadin gwiwar wata kungiya mai suna Gwagwariyya Amana.
Da yake jawabi bayan kammala rangadin, Dr Gafai ya bayyana cewa ziyarar na daga cikin muradun kungiyar wajen tabbatar da gaskiya da kuma bayyana irin kokarin Gwamna Radda ga al’ummar jihar. Ya ce aikin titin na daya daga cikin manyan ayyukan da ke nuna jajircewar gwamnan wajen farfado da tattalin arzikin jihar cikin shekaru biyu kacal da ya yi a mulki.
“Muna zuwa wuraren ne da kanmu domin tantance irin ayyukan da gwamnati ke aiwatarwa. Wannan hanyar da aka gama aiki a kanta na daya daga cikin shaidu da ke nuna ingancin mulkin Gwamna Radda,” in ji Dr Gafai.
Rangadin ya fara ne daga garin Kayauki a kan hanyar Daura, inda titin ya taso, sannan ya ci gaba har zuwa Cibiyar Kiwon Noma ta zamani (Agricultural Mechanization Centre) da ke kan hanyar Kano. Kungiyoyin sun tsaya a wurare da dama domin duba yadda aikin ya gudana da kuma tasirin sa ga al’umma.
A cewar Dr Gafai, titin zai rage cunkoson ababen hawa a birnin Katsina da kuma saukaka harkokin kasuwanci, lamarin da zai kara habaka cigaban tattalin arzikin jihar.
A karshe, Dr Musa Gafai ya bayyana cewa kungiyar Dikko Project Movement tare da hadin gwiwar abokan tafiyarta za su ci gaba da rangadi a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar domin bayyana wa jama’a irin ayyukan da gwamnatin Radda ke aiwatarwa.
“Muna da yakinin cewa da yardar Allah, kokarinmu zai tallafa wa Gwamna Radda wajen samun miliyoyin kuri’u daga birane da karkara a zaben shekarar 2027,” in ji shi.
Rangadin na daga cikin shirye-shiryen kungiyar na karfafa wayar da kan al’umma da kuma tabbatar da ganin an samu shugabanci nagari a jihar Katsina.