Kafin zuwan zaɓen 2027, dukkan 'yan Majalisar Tarayya 18 da ke wakiltar jihar Katsina wadanda suka hada da ƴan majalisar dattawa 3 da ƴan majalisar wakilai 15 sun tabbatar da goyon bayansu ga Gwamna Umar Dikko Raɗɗa don ci gaba da mulki a karo na biyu.
A wani taro da aka gudanar a Abuja ranar Alhamis da dare, Sanata Abdul'aziz Musa Yar'adua da ke wakiltar mazabar Katsina Ta Tsakiya, ya bayyana a madadin abokan aikinsa cewa sun yarda tare da hada kan su su ba da goyon baya ga Gwamna Raɗɗa a zaɓen 2027 da ke tafe.
Sanata Abdul'aziz Yar'adua ya ce wannan shawara ta samo asali ne daga nazarin yadda gwamnan ya gudanar da mulkin sa kawo yanzu da kuma goyon bayan da yake samu daga jama’a a ko’ina cikin jihar Katsina.
‘Yan majalisar sun yaba wa shugabancin Gwamna Raɗɗa, inda suka ce yana da nufin kawo ci gaba ga kowa da kowa.
Haka kuma sun bayyana jin dadin su dangane da ci gaban da aka samu a fannonin tsaro, ilimi, noma, harkokin kasuwanci da kuma dangantaka da al’umma.
Sanatan ya kuma ce, “Muna farin ciki kuma muna ganin wajibi ne mu tsaya tsayin daka wajen ba da goyon baya ga Gwamna Umar Dikko Raɗɗa don ci gaba da mulki karkashin jam’iyyar APC a zaɓen 2027. Ya nuna shugabanci na gaskiya da tawali’u. Ya yi aiki tukuru wajen tabbatar da tsaro, inganta ilimi, da kuma samar da ci gaba a fannin noma da kasuwanci a jihar Katsina.”
Ya kara da cewa, “Mun saurari muryar al’umma kuma sun nuna gamsuwa da ayyukan gwamnan.”
Shi ma a jawabin sa a madadin ƴan majalisar Wakilai, Honorable Salisu Yusuf Majigiri da ke wakiltar mazabar Mashi/Dutsi ya tabbatar da goyon bayan su ga wannan shawara.
Daga karshe ‘Yan majalisar sun yi kira ga al’ummar jihar Katsina da su hada kai wajen tallafawa Gwamna Raɗɗa domin tabbatar da ci gaba da samun nasarorin da aka fara a yanzu.