Ma’aikatar Lafiya ta Tarayya da Ta Jiha, Tare da Abokan Hulɗar su, Sun Sha Alwashin Ƙarfafa Yaƙin Maleriya
Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 18 Yuli, 2025
A wani babban mataki na ƙara ƙaimi a yaƙin kawar da cutar maleriya a Katsina, Gwamnatin Jihar ta karɓi tarin kayayyakin rigakafin cutar, ciki har da insecticide-treated nets (ITNs) sama da miliyan 4.5 da sauran kayayyakin magance cutar daga Shirin Kawar da Maleriya na Ƙasa (NMEP) da hadin gwiwar Global Fund.
Kayayyakin sun haɗa da gidan sauro (Mosquito nets) masu magani, kayan gwajin cutar maleriya da kuma magunguna, waɗanda aka samar ta hanyar tsarin saye na ƙasa tare da goyon bayan ƙungiyoyin Society for Family Health da Catholic Relief Services (CRS). An gudanar da bikin mika kayayyakin a wani taro da ya samu halartar jami’an lafiya daga matakin jiha da wakilan hukumomin lafiya na kasa da kasa.
Ms. Ayodele Shakira, wakiliyar NMEP, wadda ta wakilci shugaban shirin na ƙasa, ta miƙa gaisuwa tare da yabawa goyon bayan da Jihar Katsina ke bayarwa. “Muna farin cikin miƙa waɗannan kayayyakin kiwon lafiya da suka haɗa da gidan sauro masu magani domin tallafa wa yaƙin maleriya a jihar. An samar da su ne da kuɗaɗen Global Fund ta tsarin gwamnati,” in ji ta.
Da yake karɓar kayayyakin, Kwamishinan Lafiya na Jihar Katsina, Honorabul Musa Adamu Funtua, ya nuna gamsuwa da matakan da aka ɗauka tare da tabbatar da kudurin gwamnatin jihar wajen tabbatar da amfani da kayayyakin yadda ya dace.
“Gwamnatin jihar Katsina ta dukufa wajen ganin an cimma burin wannan gangami. Mun himmatu wajen ɗaukar nauyi da haɗin kai domin wannan aikin ya yi nasara. Wannan lokaci ne da ya dace da shiryawa sosai,” in ji Funtua.
A nasa bangaren, wakilin Catholic Relief Services (CRS), Mr. David Dedanila, ya ja hankalin al’umma da hukumomi da su tabbatar da cewa an yi amfani da kayan bisa tsari. “Duk da cewa an bayar da wadannan kayayyakin kyauta ne, an sayo su ne da harajin jama’a daga sassa daban-daban na duniya. Don haka yana da muhimmanci a tabbatar da an yi amfani da su yadda ya kamata domin yaƙar cutar maleriya,” ya jaddada.
Kayayyakin da aka karɓa sun hada da: gidan sauro guda 1,492,921 na kananan hukumomi 11 a yankin Katsina (Katsina zone) sai yankin Funtua guda 1,472,000 da yankin Daura gidan sauro (Mosquito nets guda 1,554,677
An adana su a manyan dakunan ajiya uku da ke Katsina, Funtua, da Daura, domin rabawa a cikin ƙananan hukumomi 34 da ke fadin jihar.
An bayyana cewa gangamin rabon gidan sauro na shekarar 2025 zai haɗu da shirin Seasonal Malaria Chemoprevention (SMC) domin ƙara tasiri a kan cutar. Ana sa ran fara rabon kayayyakin a makonni masu zuwa.
A karshe, an kammala bikin da mika ragamar mallakar kayayyakin daga ƙungiyoyin lafiya zuwa Gwamnatin Jihar Katsina, tare da alƙawarin ci gaba da haɗin gwiwa daga dukkan masu ruwa da tsaki.