Daga Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times, 21 ga Mayu, 2025
Jihar Katsina ce ta karɓi bakuncin babban taron Ƙasa na farko na wannan shekara da Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) ta shirya, inda manyan jami’an gwamnati daga matakan jihohi da tarayya, ƙwararru a fannin ƙididdiga da wakilan ƙungiyoyi suka hallara domin nazari da tattaunawa kan muhimmancin amfani da bayanai wajen tsara manufofi da ƙarfafa ci gaba.
Taron wanda ke gudana daga 21 zuwa 22 ga Mayu, a Hillside Royal Suite da ke birnin Katsina, ya mayar da hankali kan yadda bayanai za su iya sauƙaƙa gudanar da mulki, da ƙididdigar GDP na jihohi, da kuma gabatar da sabbin tsare-tsare na tattara bayanai.
Mataimakin Gwamnan Jihar Katsina, Faruq Lawal Jobe, wanda ya wakilci Gwamna Dikko Umar Radda, ya jagoranci bude taron. A jawabinsa, ya jaddada cewa bayanai na da muhimmanci matuƙa wajen tsara ingantattun manufofin gwamnati.
“Muna da yakinin cewa sai da bayanai masu inganci ne za mu iya samar da manufofin da za su amfanar da al’umma,” in ji Jobe, yana mai jaddada nasarorin gwamnatin jihar da suka haɗa da kafa cibiyar injinan noma da rabon takin zamani ga manoma.
Ya ƙara da cewa, gwamnatin jihar na aiki kafada da kafada da manoma wajen tabbatar da sauyin tsarin noma tare da kula da muhalli, don cimma burin samar da isasshen abinci, rage talauci da ƙirƙirar ayyukan yi.
Ɗaya daga cikin muhimman batutuwan da aka tattauna a taron shi ne kokarin Hukumar Ƙididdiga ta Ƙasa (NBS) wajen ƙididdige GDP na kowace jiha a Najeriya. Babban Jami’in Hukumar, Farfesa Prince Adeyemi Adeniran, ya bayyana cewa wannan aikin na da matuƙar muhimmanci ga masu zuba jari da masu tsara manufofin ci gaba.
“Masu zuba jari na buƙatar sanin girman tattalin arzikin kowace jiha don su iya yanke shawara cikin sauƙi,” in ji Adeniran. Ya yaba da jajircewar Jihar Katsina wajen rungumar wannan tsarin, tare da shirinta na faɗaɗa ƙididdigar GDP zuwa shekarun 2024 da 2025.
A nasa bangaren, Babban Jami’in Ƙididdiga na Jihar Katsina, Farfesa Saifullah Sani, ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta taka muhimmiyar rawa wajen bai wa sashen kididdiga tallafi, inda ya tunatar da yadda gwamnatin ta ɗauki nauyin gudanar da General Household Survey — karo na farko da haka ya faru a Najeriya.
Farfesa Sani ya kuma nuna godiyarsa ga NBS bisa haɗin gwiwa da goyon bayan da take bai wa jihar a kokarinta na samun ingantattun bayanai da ƙididdigar GDP.
Haka zalika, Farfesa Adeniran ya sanar da ƙaddamar da sabuwar dandalin dijital da ake kira (Integrated System of Administrative Statistics) (ISAS), wanda zai haɗa bayanai daga ma’aikatun gwamnati. A matakin farko, za a haɗa ma’aikatu 15 cikin tsarin, tare da shirin faɗaɗa shi nan gaba.
Bugu da ƙari, NBS za ta gudanar da zagaye na bakwai na Multiple Indicator Cluster Survey (MICS), da haɗin gwiwa da UNICEF, Tarayyar Turai da sauran abokan ci gaba, don tantance cigaban Najeriya a fannin walwalar yara da cimma burin ci gaban ƙasa (SDGs).
Mataimakin Gwamna Jobe ya kuma bayyana cewa gwamnatin jihar tana amfani da arzikin al’adu don jawo masu zuba jari. “Mun fahimci cewa al’adunmu na da matuƙar daraja a fuskar tattalin arziki,” in ji shi, yana nuni da ganawar da gwamnatin jihar ta yi da jakadun Tarayyar Turai da sauran masu sha’awar zuba jari a jihar.
A ƙarshe, taron ya buƙaci ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin hukumomin kididdiga na jihohi da na tarayya, don tabbatar da sahihan bayanai da za su inganta tsarin ci gaban ƙasa.
“Ya kamata mu mallaki hanyoyin samar da bayanai da inganta amfani da su wajen ciyar da ƙasar gaba,” in ji Farfesa Adeniran.
Taron ya nuna yadda Jihar Katsina ke ci gaba da ɗaukar matakai na gaba a fannin gudanar da mulki bisa ingantattun bayanai.