Tinubu ya umarci a cire shingayen da ke kan iyakokin Najeriya

uploads/images/newsimages/KatsinaTimes09052025_201139_FB_IMG_1746821462409.jpg



Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya kafa wani kwamitin shugaban ƙasa na musamman da zai cire dukkan wasu shingaye da ake da su a kan iyakokin ƙasar don sauƙaƙa harkokin cinikayya da tafiye-tafiye.

Amabasada Musa Nuhu wakilain Najeriya a ƙungiyar Ecowas ne ya sanar da hakan, a wata ziyara da ya kai iyakar Najeriya da Jamhuriyar Binin wato Same a ranar Laraba.

Masu ababen hawa sun sha kokawa da yadda ake karɓar kudade a hannunsu, a dukkan wani shinge da suka zo wucewa akan hanayr ta Iyakar ta Seme wato iyakar Najeriya da jamhuriyar Benin.

Ambasada Nuhu ya ce "hanyar ta kasance wadda aka fi zirga-zirga a Afrika, musamman wajen fitarwa da shigar da kaya, da shige da ficen al'umma. Zamu iya ganewa idan ana tafiye tafiye ba tare da shinge ba a yankin Afrika ta Yamma", in ji shi.

Mun ji dukkan ƙorafe-ƙorafen da ake yi kan hanyar na yadda shingayen da jami'an tsaro da na jami'an hana fasa ƙauri ke sanyawa ke shafar matafiya da kayan da masu shigowa ko fitar da kaya.

Shugaban hukumar Ecowas Omar Alieu Touray ya yi, Allah wadai kan yadda jamai'an tsaron da ke kula da shingayen da ke hanyar ke ƙarɓar kuɗi a hanun al'ummar ƙasashe daban-daban da ke shige da fice a ƙasar, wanda ya ce hakan, ya saɓa da shirin ECOWAS na haɗe yankin wuri ɗaya

BBC Hausa.

Follow Us