Zaharaddeen Ishaq Abubakar | Katsina Times
Farfesa Bichi ya bayyana manyan ci gaba da kalubalen da suka fuskanta a wa’adin mulkinsa a Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma, jihar Katsina
A wata hira ta musamman da 'yan jarida ranar Talata, 6 ga Mayu, 2025 — kwanaki kaɗan kafin ya sauka daga kujerarsa — Shugaban Jami’ar Tarayya ta Dutsin-Ma (FUDMA), Farfesa Armaya’u Hamisu Bichi, ya bayyana yadda tafiyarsa ta shugabanci jami’ar ta kasance, tare da bayyana nasarorin da aka cimma da kalubalen da suka fuskanta.
Farfesa Bichi ya fara da nuna godiya ga Allah bisa samun damar jagorantar jami’ar a matsayin Mukaddashin Shugaba na tsawon shekaru uku, kafin daga bisani a tabbatar da shi a matsayin cikakken Shugaba na tsawon shekaru biyar. Ya ce, “Tafiyar ba ta kasance mai sauƙi ba, amma tare da taimakon Allah da haɗin kan al’umma, mun samu ci gaba mai gamsarwa.”
Ya mika godiya ga tsohon Shugaban Ƙasa, Muhammadu Buhari; tsohon Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu; da tsohon Shugaban Hukumar NUC, Farfesa Abubakar Adamu Rasheed, da sauran hukumomin da suka tallafa wa ci gaban jami’ar, ciki har da TETFund.
Daga cikin manyan nasarorin da ya bayyana akwai ƙara yawan bangarorin jami’ar daga uku zuwa goma sha huɗu (14), da kuma kafa sabbin kwalejoji guda uku — Kwalejin Kimiyyar Lafiya, Kwalejin Karatun Digiri na Gaba, da Kwalejin Ci gaba da Horar da Kwararru. Ya ce wadannan kwalejoji suna karɓar ɗalibai daga sassa daban-daban na ƙasa.
Ya bayyana cewa lokacin da ya hau kujerar shugabanci, yawan ɗaliban jami’ar bai kai 5,000 ba, amma yanzu sun kai sama da 40,000. Haka kuma, daga shirye-shiryen karatu 20 da ke da lasisin cikakke guda uku kawai, yanzu jami’ar na da sama da 100, duk da sahalewar Hukumar NUC. Baya ga haka, an kafa makarantar digiri na gaba (Postgraduate School) da ke da fiye da shirye-shiryen karatu 80 masu cikakken lasisi.
A ɓangaren malamai, ya ce daga fiye da 10 da ya taras, yanzu sun haura 100. Har ila yau, fiye da mutum 100 sun kammala karatun digirin digirgir (PhD) a ƙarƙashin jagorancinsa.
Sai dai ya ce akwai buƙatar ƙarin ma’aikata domin kula da sabbin sassa da shirye-shirye da aka ƙirƙira, inda ya ce duk da cewar wasu na sukar daukar ma’aikata, hakan wajibi ne idan ana son ci gaba da ɗaukar dalibai da kuma inganta ayyuka.
Dangane da kalubalen da ya fuskanta, Farfesa Bichi ya bayyana rikicin da ya taso tsakaninsa da wasu malamai, ciki har da Farfesa Hamzat wanda ya kai shi kotu. Ya ce, “Farfesa Hamzat abokina ne, kuma ni na nada shi a mukamai da dama, amma daga bisani ya ƙalubalanci nadina a kotu, yana cewa Shugaban Ƙasa ba shi da ikon nadani.” Ya bayyana cewa a lokacin da aka naɗa shi babu Majalisar Gudanarwar jami’ar, kuma doka ta bai wa Shugaban Ƙasa ikon daukar irin wannan mataki.
Farfesa Bichi ya ce Farfesa Hamzat ya ƙi amsa gayyatar kwamitin ladabtarwa sannan ya ajiye aiki ba tare da bin dokar jami’a ba, wadda ke buƙatar sanarwar watanni shida kafin barin aiki ga malamai masu mukamin Farfesa. Saboda haka, jami’ar ta dakatar da shi tare da katse alaƙar aiki da shi daga baya.
A ƙarshe, Farfesa Bichi ya ce za a ci gaba da tuna da zamaninsa saboda ci gaban da aka samu, musamman buɗe sabbin sassa kamar su Shari’a, Likitanci da Injiniya, da kuma yadda jami’ar ta kasance abin koyi ga sauran jami’o’in da aka kafa a lokaci guda da ita.
Ya nuna alfahari da irin gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa ilimi a jihar Katsina, yankin Arewa maso Yamma da ƙasa baki ɗaya.