Cibiyar Yaƙi da Ta’addanci ta Ƙasa ta yaba wa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal kan yadda ya ke tallafa wa cibiyar,tare da ɗauki nauyin wannan shiri na cibiyar, tare da jajircewar sa wajen tabbatar da tsaron rayukan al’ummar jihar.
Wata babbar tawagar Cibiyar Yaƙi da Ta'addanci ta ziyarci gwamnan ranar Alhamis a gidan gwamnati da ke Gusau, babban birnin jihar.
Wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sulaiman Bala Idris, ya fitar ta bayyana cewa, cibiyar tana bayar da jagoranci da dabaru ga rundunar soji da sauran jami’an tsaro, da kuma hukumomin leƙen asiri kan yaƙi da ta’addanci, tare da aiwatar da aikin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro.
A nasa jawabin, Gwamna Dauda Lawal ya yaba da ziyarar da cibiyar ta kai Zamfara domin duba ƙoƙarin gwamnati na magance matsalar rashin tsaro a jihar.
“Ina yawan cewa, idan ku ka yi ƙoƙarin shawo kan Zamfara yadda ya kamata ta fuskar rashin tsaro, za ku magance kashi 80 na matsalolin tsaro a Arewa.
“Daga dukkan tsare-tsaren da na gani ya zuwa yanzu, mun mallaki abin da ake buƙata domin tunkarar waɗannan ƙalubale bisa tuntubar juna da haxin gwiwa tsakanin jihar Zamfara da ofishin mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, wannan abin a yaba ne.
“Na yi farin ciki da jin cewa Tarayyar Turai ta ware wasu kuɗaɗe, duk da cewa za mu samar da wani asusu, a Zamfara a shirye muke mu ba da tallafin, idan kun shirya gobe, mu ma mun shirya.
“Mun shirya, kuma ƙofar mu a buɗe take, duk wani abu da zai kawo sauyi mai kyau a Zamfara muna maraba da shi, muna buƙatar tsari na abin da ku ke yi domin mu ci gaba da bin diddigin lamarin, zan samu wata tawaga da za ta riƙa hulɗa da cibiyar yaƙi da ta’addanci.
Tun da farko, Shugabar Rigakafi da Yaƙi da Ta'addanci (PCVE), Ambasada Mairo Musa Abbas ta ce, tawagar ta zo jihar Zamfara ne a madadin mai baiwa shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro Mallam Nuhu Ribadu da kuma kodinetan yaƙi da ta'addanci na ƙasa, Manjo Janar Adamu Garba Laka. "Muna nan a matsayin wani bangare na dabarun bayar da shawarwari na ƙasa baki ɗaya."
“Muna son sake gode muku bisa irin karramawar da ka yi mana a Jihar Zamfara da kuma irin shugabancin da ka yi wa al’umma, muna sa ran haɗin kai don ganin cewa Zamfara ta zama kan gaba wajen yaƙi da ‘yan bindiga.”